| Hausa
AFIRKA
3 MINTI KARATU
Za mu buɗe ƙofa ga fararen hula su fice cikin aminci daga birnin El-Fasher - Rundunar RSF
Rundunar RSF ta Sudan ta ce za ta taimaka wa fararen hula waɗanda suka maƙale a cikin birnin ficewa zuwa wasu wuraren domin samun mafaka.
Za mu buɗe ƙofa ga fararen hula su fice cikin aminci daga birnin El-Fasher - Rundunar RSF
Dubban daruruwan mazauna da kuma mutanen da suka rasa matsugunansu a halin yanzu suna cikin barazanar kamuwa da yunwa, a cewar MDD. / Hoto: Reuters / Others

Rundunar RSF ta Sudan ta sanar da cewa za ta bayar da dama ga masu neman ficewa daga birnin El-Fasher na Darfur wanda ke fama da yaƙe-yaƙe tsawon makonni.

Rundunar ta RSF wadda ke yaƙi da sojojin ƙasar fiye da shekara ɗaya ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta fitar a ranar Juma’a da dare inda ta ce ta shirya taimaka wa ƴan ƙasar ficewa zuwa wasu wuraren domin neman mafaka.

El-Fasher, wanda shi ne babban birnin Arewacin Darfur, ya taɓa kasancewa ɗaya daga cikin wuraren da ke karɓar ƴan gudun hijira inda da dama daga cikinsu ke taruwa domin samun mafaka.

Dubban daruruwan mazauna da kuma mutanen da suka rasa matsugunansu a halin yanzu suna cikin barazanar kamuwa da yunwa, a cewar MDD.

Abokan juna sun zama na gaba

Dakarun na RSF sun yi kira ga mazauna El-Fasher da “su guji wuraren da ake fama da rikici da kuma wuraren da sojojin sama za su iya kai wa hari, kada su amsa munanan kiraye-kirayen da ake yi na tara jama’a da jawo su cikin yaƙi”.

Kasar Sudan dai ta shafe sama da shekara guda tana fama da rikici tsakanin sojojin ƙasar karkashin jagorancin shugaba Abdel Fattah al-Burhan da kuma RSF karkashin jagorancin tsohon mataimakinsa Mohamed Hamdan Daglo.

Rikicin ya yi sanadiyar mutuwar mutane kusan 15,000 a El-Geneina babban birnin jihar Darfur kadai, a cewar kwararrun Majalisar Dinkin Duniya.

Kungiyar agajin likitoci ta Doctors Without Borders a ranar Laraba ta ce asibitinta da ke arewacin Darfur ya karbi fiye da mutum 450 da aka kashe a fadan da aka gwabza tun ranar 10 ga watan Mayu, amma ta yi nuni da cewa, adadin wadanda suka mutu ya zarce haka.

MAJIYA:AFP
Rumbun Labarai
Tiani: Dole ne Nijar ta warware matsalolin da suka daɗe suna dabaibaye ta kafin samun nasara
Majalisar Dattawan Aljeriya ta amince da buƙatar tura sojoji zuwa Nijar
Gabon ta janye takunkumin amfani da kafafen sada zumunta bayan watanni takwas
Kenya ta tabbatar da mutuwar mutum na biyu daga cutar Ebola
Ana fargabar mutane da dama suna ƙarƙashin ɓaraguzan gini mai hawa 12 da ya rushe a Kenya
Daga Nijeriya zuwa Kenya, mutane na tsawon rai amma ba tare da cikakkiyar lafiya ba
Hamshakiyar attajira ‘yar kasar Mali ta sa sarƙar zinare mai darajar dala miliyan 1.6
Ministocin makamashi na ƙasashen ECOWAS na taro kan ajiyar batura da dokokin kasuwannin lantarki
An saki wasu mata ’yan Turai biyu da aka yi garkuwa da su a Nijar bayan shafe watanni a tsare
Nijar: Hukumomi sun ɗauki matakan tsaro na gaggawa a Agadez bayan harin da ya kashe mutum 12
Kenya ta kulla yarjejeniyar $160m ta kiyaye muhalli, da goyon bayan magadan attajiran Amurka
Ghana na shirin tunkarar Ebola bayan ɓullar cutar a Kongo DRC da Kenya da Nijeriya
Kasashe da kungiyoyin kasa da kasa na taro a Geneva don habaka kokarin samar da zaman lafiya a Sudan
Darajar kuɗin Sudan ta faɗi, inda ake canza dala ɗaya an kan fam 10,000 na ƙasar
Uganda ta musanta samun  Ebola a ƙasarta bayan wata fasinja 'yar Nijeriya ta nuna alamun cutar
Gwamnatin Nijar ta haramta fitar da man fetur da gas zuwa ƙasashen waje
Ana hasashen kuɗin da Angola za ta kashe kan tallafin fetur a 2026 zai kai dala biliyan hudu
Shugaban Masar Al-Sisi ya ce zai sauka daga mulki a 2030 ba tare da tsawaita wa'adin mulkinsa ba
Africa CDC ta ce ba a san yadda aka kashe fiye da dala miliyan 700 na kuɗin yaƙi da Ebola ba
Ya zama dole Afirka ta daina tambayar ‘me duniya za ta sayar mana’ kawai