Birnin Istanbul zai karɓi baƙuncin gasar UEFA Europa ta 2026, da gasar Conference ta 2027
Kwamitin zartarwa na hukumar UEFA ya yanke cewa za a gudanar da wasannin ƙarshe na gasar Europa ta 2026 da na Conference na 2027 a filin wasa na Besiktas da ke birnin Istanbul.
Hukumar gudanarwa ƙwallon ƙafa a Turai, ya yanke cewa za a gudanar da wasan ƙarshe na gasar Europa na 2026 a filin wasa na ƙungiyar Besiktas, wato filin Tupras Stadium da ke Istanbul.
Haka nan kuma, birnin na Istanbul zai karɓi baƙuncin wasan ƙarshe na gasar Europa Conference ta 2027.
A sanarwar da mamban kwamitin gudanarwa na UEFA, Servet Yardimci ya fitar, taron na hukumar UEFA ya gudana ne a birnin Dublin babban birnin Ireland, a Laraba.
Filin wasa na Tupras Stadium, wanda a baya ake kira da Vodafone Park, shi ne ya karɓi baƙuncin gasar UEFA Super Cup ta 2019, inda aka buga wasa tsakanin Liverpool da Chelsea.