| hausa
AFIRKA
3 MINTI KARATU
Majalisar Dokokin Kano ta soke Masarautu 5 da Gwamnatin Ganduje ta ƙirƙira
A shekarar 2019 dai aka yi wa dokar masarautu a jihar gyara inda aka ƙirƙiro ƙarin masarautu gudu huɗu masu daraja ta ɗaya a jihar.
Majalisar Dokokin Kano ta soke Masarautu 5 da Gwamnatin Ganduje ta ƙirƙira
Masarautun da aka soke su ne: Birnin Kano, Gaya, Rano, Bichi da Ƙaraye. / Hoto: TRT Afrika

Majalisar Dokokin Jihar Kano da ke arewacin Nijeriya ta soke masarautu biyar da tsohuwar gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta ƙirƙira.

Majalisar ta ɗauki matakin ne a zaman da ta yi a ranar Alhamis ɗin nan.

A jawabin da ya gabatar, shugaban masu rinjaye na majalisar, Honorabul Lawal Hussaini, ya ce majalisar ta soke dukkan "masarautu biyar da aka ƙirƙira inda za a koma tsarin Masarauta guda ɗaya kamar yadda yake tun zamanin Shehu Usmanu Ɗanfodio, don haka yanzu Kano ta zama da Sarki guda ɗaya idan gwamna ya sanya hannu."

Masarautun da aka soke su ne: Birnin Kano, Gaya, Rano, Bichi da Ƙaraye.

A shekarar 2019 dai aka yi wa dokar masarautu a jihar gyara inda aka ƙirƙiro ƙarin masarautu gudu huɗu masu daraja ta ɗaya a jihar.

Masarautun sun haɗa da Gaya da Ƙaraye da Rano waɗanda aka ɗaga darajarsu zuwa masu daraja da ta ɗaya daidai da masarautar Kano.

Sai kuma Masarautar Bichi da aka ƙirƙiro, abin da ya sa Kano ta zama tana da masarautu biyar masu daraja ta ɗaya.

A wancan lokacin, gwamnati ta yi iƙirarin cewa ta ƙirƙiro masarautun ne domin samar da ci gaba a faɗin jihar.

Sai dai a jawabinsa, mataimakin shugaban majalisar dokokin Muhammad Bello Butu Butu ya ce babu wani ci gaba da aka samu bayan ƙirƙirar masarautun.

“An gaya mana cewa idan aka kafa masarautun nan za a samar da sabbin birane da ci gaba a yankunan karkara, don hana hijira daga ƙauyuka zuwa birnin Kano. Amma ku shaida ne cewa ba mu samu wani ci gaban a zo a gani ba sakamakon ƙirƙirar masarautun nan,” in ji shi.

Masu adawa da matakin a lokacin sun soki ƙirƙiro sababbin masarautu a Kano domin a cewarsu hakan zai rusa tarihin masaratuar Kano na ɗaruruwan shekaru, inda masarautar take da ƙima a idon duniya saboda faɗinta da kuma tasirinta.

Amma mutanen yankunan da aka ƙirƙiro wa masarautun sun yi maraba da matakin, suna cewa hakan zai ƙara kawo musu ci gaba da bunƙasa.

MAJIYA:TRT Afrika
Rumbun Labarai
Mutum huɗu sun rasu bayan jiragen ruwa biyu na 'yan ci-rani sun kife a gaɓar tekun Libya
DR Congo da M23 sun cim ma yarjejeniyar zaman lafiya 'ta tarihi' a Qatar
AfDB zai ba Nijar CFA biliyan 98.7 domin magance matsalar ruwa ta shekara 70 a Zinder
MDD ta yi gargaɗi kan ƙazancewar yaƙin Sudan, ta yi kira kan barin shigar da kayan agaji
An gabatar da GH¢302bn a matsayin kasafin kuɗin Ghana na 2026 ga majalisar dokokin ƙasar
Sojojin Sudan sun daƙile harin RSF kan filin jirgin sama da dam a arewacin ƙasar
Rubio ya nemi a daina bai wa RSF makamai, ya ɗora wa rundunar laifi kan kashe-kashe a Al Fasher
Dalilin da ya sa TikTok ya goge bidiyoyi miliyan 1.5 da 'yan Uganda suka wallafa
Mutum 12 sun mutu a turmutsutsun neman aikin soja a Ghana – Rahotanni
Mahaucin Al Fasher: Yadda hotonsa ya zama alamar bakin cikin Sudan
UN Women: Mata da 'yan mata 11M suna fama da matsanancin ƙarancin abinci a Sudan sakamakon yaƙi
WHO ta bayyana damuwa kan karuwar masu ciwon siga a Afirka
Kisan kare dangi a boye da bayyane: Gushewar jinkai a Al Fasher
An ba da belin dan Gaddafi bayan da ya shafe shekaru 10 a tsare a Lebanon
Gwamnatin Trump 'ta aika wa Equatorial Guinea dala miliyan 7.5' don ta karɓi waɗanda Amurka ta kora
Ƙasashe fiye da 20 sun yi Allah wadai da RSF kan kashe-kashen da take yi a Sudan
Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya ya yi kira da a dakatar da zubar da jini a Sudan
Paul Biya na Kamaru: Dan siyasar da zai ci gaba da yin mulki har sai ya kai shekara 99?
Hare-haren RSF sun kori ƙarin dubban mutane daga Darfur da Kordofan na Sudan
RSF ta binne gawawwaki a kabarin bai-ɗaya, ta ƙone wasu domin 'ɓoye laifukan yaƙi': Likitocin Sudan