Ronaldo ya sa wa Mbappe albarka kan zuwansa Real Madrid

Cristiano Ronaldo ya aika saƙon fatan alheri ga Kylian Mbappe, wanda ya koma Real Madrid daga PSG.

By Mazhun Idris
Tun yana ƙarami Mbappe yake da burin buga wa Real Madrid wasa. Hoto: مواقع تواصل

A ƙarshe dai, tauraron ɗan wasan nan ɗan asalin Faransa, Kylian Mbappe ya koma Real Madrid ta Sifaniya. An kwashe watanni ana raɗe-raɗin zuwansa Madrid, amma sai a wannan makon ne ya tabbatar da zuwansa Madrid.

Bayan jin wannan labari ne tsohon gwarzon ɗan wasan Madrid, wanda a yanzu yake buga wa Al Nassr ta Saudiyya wasa, Cristiano Ronaldo ya aika wa Mbappe saƙon fatan alheri.

Tun asali dai, Mbappe ya ɗauki Ronaldo a matsayin abin koyinsa tun yana ƙaramin yaro mai sha'awar ƙwallo. Haka nan Mbappe bai ɓoye burinsa na son taka leda a Real Madrid ba.

Bayan kawo ƙarshen kwantiraginsa a PSG ta Faransa, Mbappe ya koma Madrid a Litinin ɗin nan, a hukumance.

Mbappe ya wallafa wani hoto a shafinsa na Instagram, inda ya nuna shi yana ƙarami sanye da rigar Madrid, da kuma hoton gwaninsa Ronaldo a bayansa. Daga nan ne Ronaldo ya amsa masa inda ya aika masa saƙon fata na gari.

Ronaldo ya yi tsokaci da cewa "Yanzu zan yi [kallo]. Ina farin cikin ganin ka haskaka Bernabeu. #HalaMadrid". Saƙon ya faranta wa dubban masoyan Madrid a faɗin duniya.

Masoyan na Madrid za su yi fatan ganin Mbappe ya bi sahun Ronaldo a Madrid, wanda ya ci ƙwallaye 450 da tallafin ƙwallo 131 a wasanni 438 da ya buga wa Madrid, kuma ya ci kofuna 16 a shekaru tara, da kyautar gwarzon duniya sau biyar.

Sai dai a yanzu Mbappe zai fara atisaye ne da tawagar ƙasar Faransa, gabanin fara gasar cin kofin ƙasashen Turai da za a yi a Jamus. Ba zai buga wa Madrid wasa ba, sai an zo wasannin sharar fage inda za su kai ziyara Amurka.