| Hausa
AFIRKA
2 MINTI KARATU
Nijeriya na gargaɗi kan cutar kwalara da ta kashe sama da mutum 30
A yayin da hukumar NCDC a ƙasar ke gargaɗi kan cutar a daidai lokacin da damuna ke kankama, gwamnatin Legas ta ce cutar ta yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 15 a bana.
Nijeriya na gargaɗi kan cutar kwalara da ta kashe sama da mutum 30
Hukumar Samar da Ruwa ta Legas ta yi gargaɗi kan shan ruwan da ba a tabbatar da tsaftar shi ba. / Hoto: Reuters / Others

Hukumomin Lafiya a Nijeriya na gargaɗi dangane da ɓarkewar cutar kwalara da ta kashe aƙalla mutum 30 a bana, akasarinsu a Legas.

Kwalara cuta ce wadda ke kama hanji wadda ke bazuwa ta hanyar gurɓataccen abinci ko ruwan sha. Tana jawo gudawa da amai da murɗawar ciki – a wani lokacin har ta yi kisa.

A wata sanarwa da Gwamnatin Legas ta wallafa a shafinta na X, ta bayyana cewa mutum 15 suka rasu zuwa yanzu a jihar inda 350 kuma aka tabbatar da sun kamu da cutar.

Hukumar Samar da Ruwa ta Legas ta yi gargaɗi kan shan ruwan da ba a tabbatar da tsaftar shi ba.

“Kamar yadda Ma’aikatar Lafiya ta Legas ta bayyana, ana alaƙanta babban dalilin da ke jawo da shan gurɓataccen ruwa da rashin tsaftar muhalli,” in ji sanarwar.

A makon da ya gabata, Hukumar Daƙile Cututtuka Masu Yaɗuwa NCDC ta gargaɗi ‘yan ƙasar dangane da ƙaruwar cutar a daidai lokacin da damuna ke ƙara kankama a ƙasar.

Hukumar ta ce aƙalla mutum 30 suka rasu tun daga farkon wannan shekarar. Wata ɓarkewar cutar da aka samu a bara ta kashe aƙalla mutum 128 sannan aka gano mutum 3,600 waɗanda ake zargin sun kamu da cutar a faɗin Afirka idan aka kwatanta da shekarar 2022 wadda aka samu mutuwar mutum biyu.

Nijeriya musamman na fama da barazanar ɓarkewar kwalara. A 2021, cutar ta kashe sama da mutum 2,300, musamman yara da ke ƙasa da shekara 14 kamar yadda hukumomin lafiya suka tabbatar.

MAJIYA:AFP
Rumbun Labarai
Ana hasashen kuɗin da Angola za ta kashe kan tallafin fetur a 2026 zai kai dala biliyan hudu
Shugaban Masar Al-Sisi ya ce zai sauka daga mulki a 2030 ba tare da tsawaita wa'adin mulkinsa ba
Africa CDC ta ce ba a san yadda aka kashe fiye da dala miliyan 700 na kuɗin yaƙi da Ebola ba
Ya zama dole Afirka ta daina tambayar ‘me duniya za ta sayar mana’ kawai
Ghana ta ware cedi 35m don farfaɗo da gandun dajin da haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida bacta ɓata
Kenya ta ƙara farashin man fetur da kashi 6 cikin 100 sakamakon rikicin Gabas ta Tsakiya
Ghana ta kama mutum 19 kan zargin laifukan intanet tare da gano damfarar dala miliyan 8.3
Nijar ta ayyana mummunan haɗarin muhalli bayan malalar mai
Gwamnatin Nijar ta kafa kwamitin magance ƙaranci da basussuka a ɓangaren man fetur
Aljeriya ta kama ‘yan Maroko 61 bisa zargin kitsa mata zagon-ƙasa
An miƙa wa 'yan kwangila ayyukan fara gina azuzuwa 357 a jihar Dosso ta Nijar
Gwamnatin Nijar ta yi watsi da buƙatar ƙarin farashin man fetur a ƙasar
MƊD: An raba mutane miliyan huɗu da gidajensu a Burkina Faso da Mali da Nijar
Sojoji na cikin mutum 71 da aka kashe a Sudan ta Kudu bayan mummunar arangama
Faransa ta kori jami’an leƙen asirin Nijar biyu daga ƙasarta
'Yar Afirka ta Kudu Navi Pillay ta ci kyautar Nobel ta Zaman Lafiya ta shekarar 2026
Rikicin wakilci a yanki: Me ke ta'azzara rikicin Ethiopia-Eritrea?
Haɗuran mota sun yi sanadin mutuwar mutum 2,151 a Ghana cikin watanni tara - Rahoton MTTD
Ethiopia ta nemi a janye dakarun Eritrea 'nan-take' daga ƙasarta
Ghana da FBI sun kama mutum 130 da ke da alaƙa da zambar $10m