'Yan bindiga sun kashe malamin jami'a a Katsina, sun sace 'ya'yansa

Rahotanni sun ce 'yan bindigar sun afka gidan malamin da tsakar dare inda suka kashe shi suka kuma sace yaransa biyu.

By Mustapha Kaita
Kashe malamin na zuwa ne mako guda bayan kashe mataimakin Shugaban Jami’ar Usman Danfodio da ke Sokoto Farfesa Yusuf Saidu. / Hoto: Others / Others

Rahotanni daga Jihar Katsina a arewacin Nijeriya na cewa ‘yan bindiga sun kashe wani malamin Jami’ar Tarayya ta Dutsinma.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a ranar Talata da tsakar dare da misalin ƙarfe 1:30 inda ‘yan bindigar suka afka gidan Dakta Tiri Gyan da ke Yarima Quarters a Ƙaramar Hukumar Dutsinma.

Mai magana da yawun ‘yan sandan Nijeriya reshen Katsina Abubakar Sadiq ya tabbatar wa kafar watsa labarai ta Channels a Nijeriyar da kisan malamin.

Waɗanda suka shaida lamarin sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun afka gidan malamin jami’ar da makamai daban-daban inda suka yi ta harbi domin tsorata mazauna rukunin gidajen.

Sun kuma bayyana cewa ɓarayin sun sace yara biyu na Dakta Gyan a lokacin da suka kai harin.

Kashe malamin na zuwa ne mako guda bayan kashe mataimakin Shugaban Jami’ar Usman Danfodio da ke Sokoto Farfesa Yusuf Saidu.

An kashe shi a lokacin da yake hanyarsa ta zuwa Kaduna daga Sokoto.