| Hausa
DUNIYA
2 MINTI KARATU
An kashe mutane da dama a hare-haren da aka kai a arewa maso yammacin Pakistan cikin sa'o'i 24: Sojoji
Hare-haren na zuwa ne a lokacin da mayakan suke sake ci gaba da kai hare-hare a yankin arewa maso yammacin kasar da ke kan iyaka da kasar Afganistan, wanda a watan da ya gabata ne gwamnatin kasar ta kaddamar da farmakin yaki da ta'addanci a yankin.
An kashe mutane da dama a hare-haren da aka kai a arewa maso yammacin Pakistan cikin sa'o'i 24: Sojoji
Wannan dai shi ne hari na biyu na ‘yan bindiga da aka sanar a cikin sa’o’i 24 a arewa maso yammacin Pakistan. / Hoto: AFP / AFP

Akalla mutane 28 da suka haɗa da fararen hula biyar da sojoji 10 da kuma wasu da ake zargin 'yan bindiga 13 ne aka kashe a hare-haren da aka kai a arewa maso yammacin Pakistan cikin sa'o'i 24 da suka gabata, a cewar wata sanarwa da rundunar sojin kasar ta fitar.

Wani harin da aka kai a wani sansanin soji da ke arewa maso yammacin Pakistan a ranar Litinin ya kashe jami’an tsaro takwas, kamar yadda rundunar sojin ta sanar a ranar Talata, bayan da wani ɗan ƙunar baƙin wake ya tayar da wata mota dauke da bama-bamai a jikin wata katanga.

Jami'an tsaro sun kashe dukkan maharan guda 10 da ke da hannu a lamarin, kamar yadda wata sanarwa da rundunar ta fitar ta faɗa.

Daga cikin wadanda suka mutu a harin na ranar Litinin har da sojoji bakwai da sojan sa-kai guda daya.

Wani hari na biyu da aka kai ranar Talata a wata cibiyar kiwon lafiya a arewa maso yammacin Pakistan ya kashe mutane bakwai da suka hada da ma'aikatan kiwon lafiya da yara da sojoji, in ji rundunar sojin kasar a ranar Talata.

An kashe dukkan mayaƙan sa kan uku a wani harin mayar da martanin da dakarun tsaro suka yi, in ji sanarwar.

Wannan dai shi ne hari na biyu na ‘yan bindiga da aka sanar a cikin sa’o’i 24 a arewa maso yammacin Pakistan.

MAJIYA:TRT World
Rumbun Labarai
Guterres na MƊD ya yaba wa yadda Turkiyya ta shirya taron COP31
Amurka ta kwashe jiragen soji daga sansanin sama na biyu a Birtaniya bayan rahoton barazanar Iran
Ƙungiyoyin ƙwadago da na ɗalibai na shirin gudanar da sabuwar zanga-zanga a Faransa
Shin Turai za ta kare ICC, ko kuwa za ta ci gaba da neman yardar Amurka?
Trump na so a kawo ƙarshen yaƙin Iran ta diflomasiyya, Netanyahu ya ce a kai ƙarin hare-hare: rahoto
Akalla 'yan Uganda 27 sun halaka ko an yanke hukuncin sun halaka a yakin Rasha da Ukraine
Hukumomin Faransa sun kama mutum 135 da ƙara dokar hana fita a wasu birane saboda zanga-zanga
Ba makawar yin Yaƙin Duniya na III in ji tsohon shugaban Serbia
Rubio ya ce taron shugabannin Amurka, Rasha da China zai amfani duniya sosai
Faransa ta hana fita a sassan Paris yayin da zanga-zangar tsadar rayuwa ta haddasa tashin hankali
Trump ya ce Qatar ta yi tayin ba shi kyautar jirgin sama samfurin 747 bayan ya nemi a ba shi aro
Gwamnatin Trump na binciken Ilhan Omar, za ta ƙwace takardarta ta ‘yar ƙasa tare da korar ta: Rahoto
An cire wani sashe na huhun Fafaroma Leo bayan yi masa tiyatar kansa - Fadar Batikan
Koriya ta Arewa ta 'harba makamai masu linzami da dama cikin tekun Japan'
Trump ya ce rashin ba shi kyautar Nobel ta Zaman Lafiya 'abin kunya ne'
Faransa ta ce za ta bai wa Saudiyya kariya a ɓangaren man fetur ɗinta
HRW: Tasa ƙeyar ’yan Ci-rani zuwa Afirka da Amurka ke yi azabtarwa ce
Trump na shirin kai wa Iran hari kafin zaɓen tsakiyar wa'adi a Amurka - rahoto
WHO ta yi kira ga Rasha da ta yi gaskiya game da rahotannin mutuwa sakamakon annobar ciwon huhu
Amurka ta janye dukka jiragen yaƙinta na B-1 daga sansanin sojin saman Birtaniya saboda tsoron hari