Morocco ta fitar da gargaɗi game da tsananin zafi a ƙasar
Tsananin zafi abu ne da aka saba gani a lokacinbazara a Moroko, amma mahukunta sun bayyana damuwa kan yadda lamarin ka iya tsananta da kuma janyo rikicin ruwan sha.
Mahukuntan Moroko na yin gargaɗi game da 'tsananin zafi' da ake sa ran fuskanta a lardunan kasar da dama a makon nan, inda darajar zafin za ta kama tsakanin 42 da 46 a ma'aunin salshiyas.
Hukumar Kula da Yanayi ta ce tun daga ranar Litinin din nan tsananin zafin zai yi tasiri a yankunan da suka hada da Tata da Zagora da Assa-Zag da Es-Semara da Errachidia.
Sauran yankunan su ne Taounate da Ouezzane da Taroudant da Sidi Kacem da Sidi Slimane da Khemisset.
Tsananin zafi abu ne da aka saba gani a Moroko, amma mahukunta sun bayyana damuwa kan yadda lamarin ka iya janyo matsalar ruwan sha.
Sauyin yanayi
Ruwan sama ya ragu da kashi 70 a shekara, in ji Ma'aikatar Ruwa da Ayyukan Noma ta Moroko a watan Janairu.
Shekaru shida a jere na fari sun bar madatsun ruwa na Moroko a cikin mummunan yanayi, wanda hakan ya janyo raguwar yankunan da ake yin noman rani a cikinsu.
Ya zuwa tsakiyar watan Janairu, madatsun ruwa na Moroko sun cika da kashi 23.2 daga kashi 31.5 a shekarar da ta gabata, in ji Ministar Ruwa, Nizar Baraka.
Mummunan farin da aka samu a shekaru goman da suka gabata ne suka sanya aka hana wanke yankuna da ruwan sha mai tsafta ko yin ban ruwa a gonaki a filayen shaƙatawa a garuruwa.
Sannan an dakatar da amfani da ban ruwan wasu gonaki da ruwan madatsun ruwan.