| Hausa
DUNIYA
6 MINTI KARATU
An yi jana'izar Haniyeh a Doha
Yaƙin da Isra'ila ke yi a Gaza ya shiga kwana na 301, kuma ya yi sanadin mutuwar Falasɗinawa aƙalla 39,480, galibinsu mata da yara tare da jikkata wasu 91,128. Sannan ana ƙiyasin wasu sama da 10,000 na binne a karkashin baraguzan gidajen da aka rusa.
An yi jana'izar Haniyeh a Doha
An rufe manya da ƙananan hanyoyi da dama da ke Doha, yayin da 'yan sanda suka ɗauki ƙarin matakan tsaro, musamman a kusa da Masallacin Imam Muhammad ibn Abd al-Wahhab, inda aka gudanar da jana'izar bayan Sallar Juma'a / Hoto: AFP / Others

Juma'a, 2 ga Agustan 2024

0945 GMT — Hukumomi a Qatar sun ɗauki tsauraran matakan tsaro a wajen jana'izar i shugaban ƙungiyar Hamas Ismail Haniyeh, wanda Isra'ila ta yi wa kisan gilla a Tehran, babban birnin Iran.

An fuskanci dogayen layuka tun daga Filin Jirgin Saman Ƙasa da Ƙasa na Hamad da ke Doha tun tsakar dare a yayin da jami'ai daga ƙasashe da dama suka isa ƙasar don halartar jana'izar.

An rufe manya da ƙananan hanyoyi da dama da ke Doha, yayin da 'yan sanda suka ɗauki ƙarin matakan tsaro, musamman a kusa da Masallacin Imam Muhammad ibn Abd al-Wahhab, inda aka gudanar da jana'izar bayan Sallar Juma'a, a cewar wakilin kamfanin dillancin labarai na Anadolu.

'Yan jarida na cikin gida da ƙasashen waje sun taru a yankin domin ɗaukar labaran jana'izar.

0446 GMT — Kisan gillar da aka yi wa shugaban Hamas ba zai taimaka wa tattaunawar tsagaita wuta ba — Biden

Shugaban Amurka Joe Biden ya ce kisan gillar da aka yi wa shugaban Hamas Ismail Haniyeh bai taimaka wa tattaunawar tsagaita wuta a yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza ba.

An samu ƙaruwar zaman ɗarɗar a yaƙin da ake yi a Gabas ta Tsakiya bayan kisan gillar da aka yi wa Haniyeh a Iran inda ake fargabar ramuwar gayya kan Isra'ila.

Hamas da rundunar zaratan sojojin Iran ta Revolutionary Guard sun tabbatar da kisan Haniyeh, wanda yake shiga tsakani a tattaunawar tsagaita wuta a Gaza.

"Ba zai taimaka wa tattaunawar ba," in ji Biden a tattaunawa da manema labarai yayin da suka tambaye shi kan ko kisan Haniyeh zai tarwatsa tattaunawar tsagaita wuta.

Kazalika Biden ya ce ya tattauna da Firaministan Benjamin Netanyahu ranar Alhamis.

2145 GMT — Biden ya sha alwashin goyon bayan Netanyahu bayan harin makamai masu linzami da Hezbollah ta kai Isra'ila

Shugaban Amurka Joe Biden ya tattauna da firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, yayin da Fadar White House ta fada a cikin wa jawabi cewa, Biden "ya jaddada aniyarsa na tabbatar da tsaron Isra'ila daga duk wata barazana daga Iran," ciki har da ƙawayenta Hamas da Hezbollah da Houthi.

Ita ma mataimakiyar shugaban kasa Kamala Harris ta halarci kiran wayar.

Biden ya kuma tattauna kan kokarin tallafa wa tsaron Isra'ila da kuma muhimmancin rage zaman ɗar-ɗar a yankin, duk da cewa ba a yi ƙasa a gwiwa ba wajen kisan kiyashin da Isra'ila ke yi a Gaza da kuma kashe-kashen da ake yi a yankin da ya ƙara ruruta wutar rikicin yankin.

A cewar Cibiyar Bayar da Bayanai ta Armed Conflict Location and Event Event (ACLED), Isra'ila ce ke da alhakin kai hare-hare 17,081 a kasashe takwas tun daga ranar 7 ga watan Oktoban bara, ciki har da yankin Falasdinu da ta mamaye da Lebanon da Syria da Masar da Yemen da Jordan da Iran da kuma Iraƙi.

2000 GMT — An nemi Biden ya kawo ƙarshen shirun da ake yi kan yadda Isra'ila ke ƙwace yankuna da kisan kiyashi a Gaza

Majalisar Hulda da Musulman Amurka, CAIR, kuma babbar kungiyar kare hakkin Musulmai a Amurka, ta ce tilas ne gwamnatin Biden ta dauki mataki bayan da Isra’ila ta sanar da sake ƙwace kasar Falasdinu a Yammacin Gabar Kogin Jordan da ta mamaye tare da kashe wasu fararen hula a Gaza.

Isra'ila ta sanar da ƙwace kusan kadada 2,000 ta kasar Falasdinu kusa da garin Salfit da ke Gabar Yammacin Kogin Jordan da ta mamaye.

"Ci gaba da yin shiru da gwamnatin Biden ke yi kan kisan kiyashin da ake yi a kullum da sauran laifukan yaki a Gaza, da kuma batun mamaye Yammacin Kogin Jordan, yana aike wa da gwamnatin Isra'ila mai tsattsauran ra'ayi cewa ba za ta taba daukar alhakin duk wani mataki da ta dauka ba, komai rashin dacewarsa a doka, "in ji Mataimakin Daraktan CAIR na kasa Edward Ahmed Mitchell.

"Dole a kawo ƙarshen wannnan shirun na kisan ƙare dangi."

MAJIYA:TRT Afrika da abokan hulda
Rumbun Labarai
Faransa ta hana fita a sassan Paris yayin da zanga-zangar tsadar rayuwa ta haddasa tashin hankali
Trump ya ce Qatar ta yi tayin ba shi kyautar jirgin sama samfurin 747 bayan ya nemi a ba shi aro
Gwamnatin Trump na binciken Ilhan Omar, za ta ƙwace takardarta ta ‘yar ƙasa tare da korar ta: Rahoto
An cire wani sashe na huhun Fafaroma Leo bayan yi masa tiyatar kansa - Fadar Batikan
Koriya ta Arewa ta 'harba makamai masu linzami da dama cikin tekun Japan'
Trump ya ce rashin ba shi kyautar Nobel ta Zaman Lafiya 'abin kunya ne'
Faransa ta ce za ta bai wa Saudiyya kariya a ɓangaren man fetur ɗinta
HRW: Tasa ƙeyar ’yan Ci-rani zuwa Afirka da Amurka ke yi azabtarwa ce
Trump na shirin kai wa Iran hari kafin zaɓen tsakiyar wa'adi a Amurka - rahoto
WHO ta yi kira ga Rasha da ta yi gaskiya game da rahotannin mutuwa sakamakon annobar ciwon huhu
Amurka ta janye dukka jiragen yaƙinta na B-1 daga sansanin sojin saman Birtaniya saboda tsoron hari
Trump ya yi gargaɗin cewa yaƙi da Iran zai zo ƙarshe ko ta halin ƙaƙa 'nan ba da jimawa ba’
An ceto baƙin-haure 260 a gaɓar tekun Mauritania
Sau takwas sojojin Amurka na yunƙurin kashe kansu a cikin USS Abraham Lincoln, in ji gwamnatin Trump
Kwamitin Zaman Lafiya na Duniya zai gabatar da shirin farfado da Gaza na dala biliyan $2.45: Rahoto
Erdogan a UNGA: Gaza ce sansanin tsare mutane mafi muni da rashin tausayi da abin kunya a zamaninmu
Trump ya yi wa Iran barazana, ya kira ICC ‘marar gaskiya‘, ya sauya sunan AI zuwa ‘SI’
Amurka ta kai 'yan ci-rani fiye da 25,000 da ta kora zuwa ƙasashen da ba su da alaƙa da su: Bincike
Antonio Guterres ya nemi a bai wa Afirka kujerun dindindin a Kwamitin Tsaro na MDD
Trump ya sa hannu kan sabuwar dokar takunkumi ga Rasha: China da India na iya fuskantar sabon haraji