| Hausa
AFIRKA
3 MINTI KARATU
Jami'an tsaron Nijeriya sun far wa hedkwatar NLC a Abuja
A ranar Laraba da misalin karfe 8:30 na dare gomman jami’an tsaro ɗauke da makamai sun far wa ginin hedkwatar ƙungiyar ƙwadago wato Labour House inda suka yi awon-gaba da wasu takardu, a cewar wata sanarwa da  NLC ta fitar a Alhamis.
Jami'an tsaron Nijeriya sun far wa hedkwatar NLC a Abuja
NLC ta buƙaci gwamnatin Nijeriya ta gaggauta janye jami’an tsaro daga hedikwatar ta, inda ta ce dole a kawo ƙarshen wannan cin zali.''/ Hoto: Reuters / Others

Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa a Nijeriya (NLC) ta bayyana cewa jami’an tsaro ɗauke da muggan makamai sun yi dirar-mikiya a hedikwatarta da ke Abuja wato Labour House.

''A ranar Laraba da misalin karfe 8:30 na dare gomman jami’an tsaro ɗauke da makamai sun kai wa ginin Labour House hari,'' a cewar wata sanarwa da NLC ta fitar a safiyar Alhamis.

''Gomman jami'an tsaro sanye da kayan soja da na gida sun kai hari Labour House inda suka kutsa kai a hawa na biyu da na goma kana suka yi awon-gaba da wasu takardu a cikin motocinsu, suna ikirarin cewa wai ana amfani da takardun wajen rura wutar zanga-zangar da ake yi Nijeriya.''

''Jami'an sun kwashe ɗaruruwan litattafai da sauran maƙaloli," in ji sanarwar da ke ɗauke da sa hannun shugaban sashen yaɗa labarai da hulɗa da jama'a na NLC, Benson Upah ya fitar.

"Jami'an tsaron sun yi ikirarin cewa suna neman wasu takardu da kayayyaki da aka yi amfani da su wajen rura wutar zanga-zangar #EndBadGoveranance da ake yi a Nijeriya."

Kawo yanzu dai ƙungiyar NLC ba ta kai ga tantance yawan abubuwan da jami'an suka kwashe daga ofishinta ba.

Kazalika NLC ta buƙaci gwamnatin Nijeriya ta gaggauta janye jami’an tsaro daga hedikwatar ta, inda ta ce dole a kawo ƙarshen wannan cin zali.''

Lamarin dai ya faru adaidai lokacin da 'yan Nijeriya suke ci gaba da gudanar da zanga-zangar kwana 10 kan neman a kawo ƙarshen tsadar rayuwa a ƙasar, inda a yau aka shiga kwana ta kakwas.

MAJIYA:TRT Afrika
Rumbun Labarai
Burhan na Sudan ya buƙaci a cire siyasa a rabon tallafin yaƙi da sauyin yanayi ga ƙasashe mara ƙarfi
Greenpeace ta gargaɗi Ghana kan barazanar shara sakamakon shigo da tsofaffin tufafi miliyan 1 a mako
Yadda El Niño ke sake haifar da ɓarkewar cutar Zazzaɓin Rift Valley a Gabashin Afirka
BAMEX 2026: An fara baje-kolin fasahar tsaro ta ƙasa da ƙasa a Mali
Kotu a DR Congo ta yanke wa sojoji 66 hukuncin kisa saboda 'ja da baya a fagen daga'
Kwale-kwale dauke da ‘yan ci-rani ya kife a kusa da Senegal, mutum 21 sun rasu, in ji hukumomi
An yanke wa jagoran ƙungiyar asiri a Kenya hukuncin ɗaurin shekara 200 kan kisan yara 190
MƊD ta yi gargaɗin cewa El Nino za ta iya raba mutum miliyan uku da gidajensu a Gabashin Afirka
Shugaban Nijar Tiani ya karɓi baƙuncin takwaransa na Mali Assimi Goita a Yamai
Farashin burodi ya ninka cikin mako ɗaya a Sudan sakamakon ƙarancin fetur da fulawa
Ethiopia da Sudan sun rufe ofisoshin jakadancin juna bayan zarge-zargen tsoma baki a yaƙin basasa
Shugaban Benin ya sauya manyan hafsoshin soji bayan kusan shekara ɗaya da yunƙurin juyin mulki
Dangote ya ƙaddamar da aikin wajen adana man fetur na dala biliyan 2.5 a Namibia
Afirka ta Kudu ta tuhumi mutum biyu saboda satar fiye da dala dubu 580 a gonar Shugaba Ramaphosa
Ghana ta ƙwato fiye da cedi biliyan 18 ta hanyar binciken kuɗi – Babbar mai binciken kuɗi
Sojojin Sudan sun ce sun dakile hare-haren RSF a yankin Kogin Nilu
Wakilan musamman na China za su ziyarci Afirka don tattaunawar zaman lafiyar yanki
Nijar ta karɓi tankokin dakon man fetur 53 daga Aljeriya domin rage matsalar karancin mai
Ayarin motocin sojin Aljeriya ya isa birnin Arlit na Nijar
Saudiyya ta dakatar da shiga kasar daga Kenya saboda Ebola