| Hausa
DUNIYA
6 MINTI KARATU
Umarnin da Isra'ila ta bayar na ficewa a Gaɓar Yamma ya saɓa dokokin duniya — Hamas
Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza, wanda ya shiga kwana na 327, ya kashe Falasɗinawa aƙalla 40,476— galibinsu mata da yara — tare da jikkata fiye da mutum 93,647, sannan an yi amanna cewa ɓaraguzan gine-gine sun danne fiye da mutum 10,000.
Umarnin da Isra'ila ta bayar na ficewa a Gaɓar Yamma ya saɓa dokokin duniya — Hamas
Sojojin Isra'ila sun ƙaddamar da gagarumin kutsen soja a arewacin Gaɓar Yamma ciki har da biranen Jenin da Tikarem da Tubas, inda kawo yanzu aka kashe Falasɗinawa 11 /  Hoto: AA / Photo: AFP / AFP

Laraba, 28 ga watan Agusta 2024

Ƙungiyar gwagwarmaya ta Falasɗinawa Hamas ta yi tir da kiran da Isra’ila ta yi na a ba da umarnin ficewa a Gaɓar Yamma da aka mamaye irin yadda ake yi wa Falasɗinawa a Gaza, abin da ta ce “ya saɓa wa dokokin duniya.”

Ministan Harkokin Ƙasashen Waje na Isra’ila Katz ya yi kira da a a yi wa Falasdinawa a arewacin Gaɓar Yamma, kamar yadda ake yi a Gaza, har da ficewa daga gidaje.

“(Wannan) kira ne na zalunci don faɗaɗa irin ɓarnar da ake yi, da kisan kiyashi, da ƙoƙarin ƙarar da Falasɗinawa,” kamar yadda Shugaban Hamas Izzat al Rishaq ya faɗa a cikin wata sanarwa.

“Kiran ya nuna irin yadda Isra’ila ke matuƙar saɓa dokokin duniya, kuma abin na nuna irin yadda shugabannin gwamnatin ke cin karensu ba babbaka, waɗanda suke kauce wa duk wani hukunci kan yadda suke cin zarafin ɗan adam.”

Shugaban Hamas ya yi kira ga ƙasashen duniya da Majalisar Ɗinkin Duniya su yi “gaggawar janye duk wata kariya da gwamnatin Amurka ke samar wa masu aikata laifukan yaƙi na Isra’ila.

1500 GMT — Masar ta yi Allah wadai da aikin soja a biranen Gaɓar Yamma

Masar ta yi Allah wadai da farmakin da Isra’ila ta yi a biranen da aka mamaye a arewacin Gabar Yamma.

A cikin wata sanarwa, Ma’aikatar Harkokin Wajen Isra’ila ta ce tana ɗaukar farmakin da Isra’ila ke yi a biranen Falasɗinawa da aka mamaye a Gaɓar Yamma “a matsayin ci gaba da saɓa dokokin duniya, da dokokin jin ƙai na duniya, da yarjeniyoyin Geneva guda hudu wacce ta kare haƙkoƙin mutanen da suke ƙarƙashin mamaye.”

“Masar na ganin wannan matakin a matsayin matakin faɗaɗa yaƙi da fito-na-fito a yankunan falasɗinawa,” a cewar sanarwar.

Ta yi kira da “a ɗauki matakai na bai-ɗaya kuma masu tasiri don kare Falasɗinawa ya kuma kawo ƙarshen ci gaba da kai hare-hare kan fararen hula da ba sa ɗauke da makamai, da sanya takunkumi da ƙwace kadarori.” Masar ta kuma yi gargadin “mummunan sakamako” da za a iya samu daga ayyukan da Israi’la ke yi.

0726 GMT — Ministan harkokin wajen Isra'ila ya yi barazanar tursasawa a kwashe Falasɗinawa daga yankunan arewa da Gaɓar Yammacin Kogin Jordan a yayin da suke ci gaba da kutsawa yankin.

Tun da farko rundunar sojin Isra'ila ta ƙaddamar da samame a yankunan arewa da Gaɓar Yammacin Kogin Jordan, da suka haɗa da biranen Jenin, Tulkarem da Tubas, inda kawo yanzu suka kashe Falasɗinawa 11.

A sanarwar da ya wallafa a shafin X, Israel Katz ya ce sojojin ƙasarsu suna aiki a Jenin da Tulkarem domin daƙile abin da ya bayyana "ayyukan 'yan ta'adda a kan Isra'ila a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan."

Ya ƙara da cewa samamen da sojoji suka kai ya haɗa da "kwashe Falasɗinawa mazauna yankunan arewa da Gaɓar Yammacin Kogin Jordan na ɗan wani lokaci" kamar yadda suka yi a Gaza.

0418 GMT —Isra'ila ta kashe Falasɗinawa da dama a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan

Isra'ila ta kashe Falasɗinawa aƙalla goma a hare-hare ta sama da samame da ta kai a wasu garuruwa da ke arewa da Gaɓar Yammacin Kogin Jordan, a cewar mai magana da yawun ƙungiyar bayar da agaji ta Red Crescent.

Jiragen yaƙin Isra'ila sun kashe Falasɗinawa biyu a birnin Jenin, da kuma mutum huɗu a wani ƙauye da ke maƙotaka da birnin, da mutum huɗu a wani sansanin 'yan gudun hijira da ke kusa da garin Tubas, in ji Ahmed Jibril, jami'in ƙungiyar bayar da agajin.

0123 GMT — Shugaban Falasɗinawa da Yarima Mai Jiran Gadon Sarautar Saudiyya sun tattauna kan yaƙin Isra'ila a Gaza

Shugaban Falasɗinawa Mahmoud Abbas da Yarima Mai Jiran Gadon Sarautar Saudiyya Mohammed bin Salman sun gana a Riyadh inda suka tattaunawa kan yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza da aka mamaye.

Yayin ganawar tasu, Abbas da Bin Salman sun yi waiwaye kan halin da Falasɗinawa suka faɗa a ciki da kuma yanayin da yankin Gabas ta Tsakiya yake ciki. Kazalika sun tattauna kan yunƙurin Falasɗinawa da ƙasashen Larabawa na ganin Isra'ila ta daina kai hare-hare kan Falasɗinawan Gaza da Gaɓar Yammacin Kogin Jordan, ciki har da Birnin Ƙudus.

Shugaba Abbas ya yi gargaɗi game da hatsarin kalaman da Isra'ila ta yi game da yiwuwar mamaye wurare masu tsarki na Musulmai da Kiristoci, musamman kalamin da Ministan Tsaron Ƙasar mai tsattsauran ra'ayi Itamar Ben-Gvir ya yi cewa za su gina wurin bautar Yahudawa a cikin Masallacin Ƙudus, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Falasɗinu (WAFA) ya rawaito.

MAJIYA:TRT World
Rumbun Labarai
Faransa ta hana fita a sassan Paris yayin da zanga-zangar tsadar rayuwa ta haddasa tashin hankali
Trump ya ce Qatar ta yi tayin ba shi kyautar jirgin sama samfurin 747 bayan ya nemi a ba shi aro
Gwamnatin Trump na binciken Ilhan Omar, za ta ƙwace takardarta ta ‘yar ƙasa tare da korar ta: Rahoto
An cire wani sashe na huhun Fafaroma Leo bayan yi masa tiyatar kansa - Fadar Batikan
Koriya ta Arewa ta 'harba makamai masu linzami da dama cikin tekun Japan'
Trump ya ce rashin ba shi kyautar Nobel ta Zaman Lafiya 'abin kunya ne'
Faransa ta ce za ta bai wa Saudiyya kariya a ɓangaren man fetur ɗinta
HRW: Tasa ƙeyar ’yan Ci-rani zuwa Afirka da Amurka ke yi azabtarwa ce
Trump na shirin kai wa Iran hari kafin zaɓen tsakiyar wa'adi a Amurka - rahoto
WHO ta yi kira ga Rasha da ta yi gaskiya game da rahotannin mutuwa sakamakon annobar ciwon huhu
Amurka ta janye dukka jiragen yaƙinta na B-1 daga sansanin sojin saman Birtaniya saboda tsoron hari
Trump ya yi gargaɗin cewa yaƙi da Iran zai zo ƙarshe ko ta halin ƙaƙa 'nan ba da jimawa ba’
An ceto baƙin-haure 260 a gaɓar tekun Mauritania
Sau takwas sojojin Amurka na yunƙurin kashe kansu a cikin USS Abraham Lincoln, in ji gwamnatin Trump
Kwamitin Zaman Lafiya na Duniya zai gabatar da shirin farfado da Gaza na dala biliyan $2.45: Rahoto
Erdogan a UNGA: Gaza ce sansanin tsare mutane mafi muni da rashin tausayi da abin kunya a zamaninmu
Trump ya yi wa Iran barazana, ya kira ICC ‘marar gaskiya‘, ya sauya sunan AI zuwa ‘SI’
Amurka ta kai 'yan ci-rani fiye da 25,000 da ta kora zuwa ƙasashen da ba su da alaƙa da su: Bincike
Antonio Guterres ya nemi a bai wa Afirka kujerun dindindin a Kwamitin Tsaro na MDD
Trump ya sa hannu kan sabuwar dokar takunkumi ga Rasha: China da India na iya fuskantar sabon haraji