| Hausa
AFIRKA
2 MINTI KARATU
Daliban Jam'iar Benin da dama sun maƙale bayan rushewar gini a Edo
Ɗaya daga cikin ɗaliban da ke wurin da lamarin ya faru ya bayyana cewa wasu masu aikin ceto na jami’ar ta Benin sun ceto wasu da suka maƙale inda nan take aka kai su asibiti.
Daliban Jam'iar Benin da dama sun maƙale bayan rushewar gini a Edo
Ana yawan samun matsalolin rushewar gine-gine a Nijeriya inda ƙwararru suke dangana shi da rashin aiwatar da ka'idojin gini, da sakaci da kuma amfani da kayayyaki marasa inganci. / Hoto: Others / Others

Ɗalibai da dama na Jami’ar Benin sun maƙale a cikin wani gini mai hawa uku da ya rushe a Jihar Edo da ke Nijeriya.

Ginin wanda ke a Ekosodin, ya rushe ne da safiyar Asabar.

Rahotanni sun ce ginin ya rushe bayan an yi wani ruwa mai ƙarfi da safiyar ta Asabar.

Ekosodin na da iyaka da Jami’ar Benin, kuma yankin na da ɗalibai da dama da ke zaune.

Rahotanni sun ce duk da cewa har yanzu akwai wasu ɗalibai da ke maƙale, amma akwai waɗanda aka samu nasarar cetowa.

Ɗaya daga cikin ɗaliban da ke wurin da lamarin ya faru ya bayyana cewa wasu masu aikin ceto na jami’ar ta Benin sun ceto wasu da suka maƙale inda nan take aka kai su asibiti, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

Ana yawan samun matsalolin rushewar gine-gine a Nijeriya inda ƙwararru suke dangana shi da rashin aiwatar da ka'idojin gini, da sakaci da kuma amfani da kayayyaki marasa inganci.

Ko a kwanakin baya sai da aƙalla ɗalibai 22 suka mutu bayan ginin wata makaranta da ke tsakiyar birnin Jos ya rufta a kan ɗaliban da ke rubuta jarrabawa.

Aƙalla mutum 45 ne suka mutu a shekarar 2021 bayan da wani dogon bene da ake ginawa ya ruguje a gundumar Ikoyi da ke babban birnin tattalin arzikin Nijeriyar, Legas. S

annan mutum 10 ne suka mutu sakamakon ruftawar wani gini mai hawa uku a unguwar Ebute-Metta da ke Legas shekara guda bayan haka.

MAJIYA:TRT Afrika
Rumbun Labarai
Tiani: Dole ne Nijar ta warware matsalolin da suka daɗe suna dabaibaye ta kafin samun nasara
Majalisar Dattawan Aljeriya ta amince da buƙatar tura sojoji zuwa Nijar
Gabon ta janye takunkumin amfani da kafafen sada zumunta bayan watanni takwas
Kenya ta tabbatar da mutuwar mutum na biyu daga cutar Ebola
Ana fargabar mutane da dama suna ƙarƙashin ɓaraguzan gini mai hawa 12 da ya rushe a Kenya
Daga Nijeriya zuwa Kenya, mutane na tsawon rai amma ba tare da cikakkiyar lafiya ba
Hamshakiyar attajira ‘yar kasar Mali ta sa sarƙar zinare mai darajar dala miliyan 1.6
Ministocin makamashi na ƙasashen ECOWAS na taro kan ajiyar batura da dokokin kasuwannin lantarki
An saki wasu mata ’yan Turai biyu da aka yi garkuwa da su a Nijar bayan shafe watanni a tsare
Nijar: Hukumomi sun ɗauki matakan tsaro na gaggawa a Agadez bayan harin da ya kashe mutum 12
Kenya ta kulla yarjejeniyar $160m ta kiyaye muhalli, da goyon bayan magadan attajiran Amurka
Ghana na shirin tunkarar Ebola bayan ɓullar cutar a Kongo DRC da Kenya da Nijeriya
Kasashe da kungiyoyin kasa da kasa na taro a Geneva don habaka kokarin samar da zaman lafiya a Sudan
Darajar kuɗin Sudan ta faɗi, inda ake canza dala ɗaya an kan fam 10,000 na ƙasar
Uganda ta musanta samun  Ebola a ƙasarta bayan wata fasinja 'yar Nijeriya ta nuna alamun cutar
Gwamnatin Nijar ta haramta fitar da man fetur da gas zuwa ƙasashen waje
Ana hasashen kuɗin da Angola za ta kashe kan tallafin fetur a 2026 zai kai dala biliyan hudu
Shugaban Masar Al-Sisi ya ce zai sauka daga mulki a 2030 ba tare da tsawaita wa'adin mulkinsa ba
Africa CDC ta ce ba a san yadda aka kashe fiye da dala miliyan 700 na kuɗin yaƙi da Ebola ba
Ya zama dole Afirka ta daina tambayar ‘me duniya za ta sayar mana’ kawai