UNICEF ta nuna damuwa kan yadda Isra'ila ta kashe yara 24 a Lebanon
"Na damu matuka da yadda ake ci gaba da kai hare-hare a Lebanon da Isra'ila, wanda a safiyar yau aka bayar da rahoton mutuwar akalla yara 24 a kudancin kasar ta Lebanon," kamar yadda daraktar UNICEF Catherine Russell ta bayyana
Daraktar Asusun Kula da Ƙananan Yara ta Majalisar Ɗinkin Duniya Catherine Russell ta nuna matuƙar damuwa dangane da yadda rikici ke ƙara ƙaruwa a Lebanon da Isra’ila, musamman bayan wani rahoto da ya nuna cewa wani hari ya kashe aƙalla yara 24 da ke zaune a kudancin Lebanon a ranar Litinin.
"Na damu matuka da yadda ake ci gaba da kai hare-hare a Lebanon da Isra'ila, wanda a safiyar yau aka bayar da rahoton mutuwar akalla yara 24 a kudancin kasar ta Lebanon," in ji ta, tana mai jaddada cewa tashin hankalin na nuni da wani "ƙaruwar hatsari " ga fararen hula a yankin.
Ta yi nuni da cewa, yara a Labanon da Isra'ila na fama da matsananciyar damuwa saboda ci gaba da kai hare-hare ta sama da kuma hijira da suke yi daga gidajensu.
Russell ta bukaci dukkan bangarorin da abin ya shafa da su kiyaye haƙƙin da ya rataya a wuyansu karkashin dokar jin kai ta kasa da kasa don kare fararen hula, ababen more rayuwa, ma'aikatan jin kai, da ma'aikatan lafiya.
Isra'ila ta kaddamar da hare-hare ta sama a kudanci da gabashin Lebanon, inda hukumomin lafiya na kasar Lebanon suka ce akalla mutum 492 ne suka mutu, ciki har da kananan yara 35, yayin da wasu 1,645 suka jikkata a hare-haren da aka kai tun safiyar ranar Litinin, wanda kuma ya tilasta wa dubban fararen hula tserewa daga gidajensu.
Kungiyar Hezbollah da Isra'ila dai na ci gaba da gwabza fada a kan iyakokin ƙasashen tun bayan da Isra’ilar ta ƙaddamar da yaƙi a Zirin Gaza, wanda ya yi sanadin mutuwar mutum sama da 41,400, wadanda akasarinsu mata da kananan yara ne.
Sojojin Isra’ila sun ci gaba da matsa ƙaimi inda suke kai hare-hare a Lebanon, tare da yin kunnen uwar shegu da gargaɗin da ƙasashen duniya ke yi kan cewa yaƙin na Gaza zai iya bazuwa zuwa ga sauran yankuna.