AFIRKA
3 MINTI KARATU
Kwalara ta ɓarke a Borno, makonni bayan ambaliyar ruwa
Hukumomin lafiya a jihar ta Borno da ke arewa maso gabashin Nijeriya sun ce fiye da mutane 450 ne da ambaliyar ta raba da muhallansu ake zargin sun kamu da cutar kwalara.
Kwalara ta ɓarke a Borno, makonni bayan ambaliyar ruwa
Cibiyar Yaƙi da Cututtuka ta Nijeriya NCDC ta ce fiye da mutane 10,000 ne suka kamu da cutar ta kwalara a ƙasar, yayin da kusan 360 suka mutu. / Hoto: Reuters
6 Oktoba 2024

Kwalara ta ɓarke a jihar Borno da ke arewacin Nijeriya, makonni bayan mummunar ambaliyar ruwa da ta mamaye birnin Maiduguri, a cewar Ƙungiyar Likitoci ta jihar.

Ambaliyar ruwan ta lalata tsarin kula da tsaftar muhalli da cibiyoyin samar da ruwan sha.

Shugaban Ƙungiyar Likitocin Elyakub Yakubu Mohammed ya ce an samu mutane 451 da ake zargin sun kamu da cutar, daga cikin dubban mutanen da ambaliya ta raba da muhallansu, inda aka tabbatar da mutane 128 sun kamu bayan an yi musu gwaji.

Ya kara da cewa sai dai an gano mutane 20 da ba su kamu da cutar ba daga cikin waɗanda aka yi wa gwajin.

Shugaban na ƙungiyar likitoci ya yi kira ga hukumomi su ƙarfafa tsarin samar da ruwan sha da tsaftar muhalli, su kuma ƙaddamar da gagarumin shirin riga-kafi, sannan a duƙufa wajen wayar da kan jama'a.

A ranar Juma'ar da ta gabata Kwamishinan Lafiya na jihar ta Borno Baba Mala Gana ya bayyana cewa cutar ta kwalara ta bazu zuwa wasu yankuna huɗu na jihar, bayan mummunar ambaliyar ruwa da aka fuskanta.

Hukumomi a Nigeria sun ce mutane 359 aka tabbatar da mutuwarsu sakamakon kamuwa da cutar a jihohin ƙasar 36 har da Abuja, babban birnin ƙasar.

Cibiyar Yaƙi da Cututtuka ta Nijeriya NCDC ta kuma ce fiye da mutum 10,000 ne suka kamu da cutar a faɗin ƙasar zuwa ƙarshen makon jiya.

NCDC ta ce matsalar na ƙara ta'azzara tun lokacin da aka fara fuskantar mamakon ruwan sama a damunar bana.

Ta ce rashin tsaftar muhalli da tsaftataccen ruwan sha da kuma yadda mutane suke yin ba-haya a waje, su ne muhimman abubuwan da ke ƙara yaɗa cutar.

MAJIYA:TRT Afrika
Rumbun Labarai
Hatsarin mota ya yi ajalin fiye da mutum 1,000 a Nijar a shekarar 2023, fiye da 12,000 sun jikkata
Sabbin hotunan tauraron dan'adam sun gano alamun 'kaburburan bai-daya a El-Fasher a Sudan
MDD ta yi gargaɗin cewa yaƙin Sudan na gurgunta tattalin arzikin Sudan ta Kudu
Trump ya ce bai kamata Afirka ta Kudu ta kasance cikin G20 ba, ba zai je taronta a Johannesburg ba
'Yan Sudan sun ba da mummunan labarin yi wa mata fyade yayin da suke tserewa daga Al Fasher
An kashe mutane 40 a harin da aka kai wa taron jana'iza a yankin Kordofan na Sudan: MDD
Yadda biranen Afirka mafiya tsafta suke bayyana sauyin da ake samu a nahiyar
Sojojin Ruwa na Ghana sun kama ‘yan Nijeriya 10 da suka ɓuya a jirgin ruwan Panama a Tema
Harin jirgin sama maras matuƙi na RSF ya kashe mutane da dama a lardin Kordofan na Arewa a Sudan
Fiye da mutum 1,500 sun rasa matsugunansu a Sudan sakamakon taɓarɓarewar tsaro: MDD
Dakarun RSF sun kashe mata 300, sun yi wa 25 fyaɗe cikin awa 48 a Al Fasher – Minista
Amurka ta buƙaci a tattauna domin kawo ƙarshen yaƙin Sudan, ba amfani da ƙarfin soja ba
Ana fargabar dubban mutane na cikin 'mummunan hatsari' a birnin Al Fasher na Sudan da RSF ta ƙwace
Shugabar Tanzania Samia Hassan ta lashe zaɓen ƙasar da kashi 97.66 cikin 100
Tchiroma Bakary: Sojojin Kamaru sun yi wa jagoran 'yan adawar kasar rakiya zuwa wuri mai 'aminci'
Kudirin 1325 ya cika shekara 25: Me ya sa dole Afirka ta jagoranci samar da zaman lafiya a duniya
Dubban mutane sun tsere daga North Kordofan yayin da RSF ta zafafa kai hari a yankin Darfur na Sudan
Fararen-hula 177,000 sun maƙale a Al Fasher na Sudan, yayin da RSF ke ci gaba da kisa - Likitoci
Rundunar RSF ta amsa aikata 'take haƙƙi' a Al Fasher na Sudan
Kenya ta tabbatar da mutuwar mutum 11 'yan yawon bude ido a hatsarin jirgin da aka yi a kasar