| Hausa
DUNIYA
3 MINTI KARATU
Lebanon ta buƙaci MDD ta tilasta wa Isra'ila ta dakatar da kai hari ta kuma janye dakarunta
Yaƙin da mahukuntan Tel Aviv suka kwashe fiye da shekara ɗaya suna yi a Gaza ya kashe Falasɗinawa aƙalla 42,409. A gefe guda, hare-haren da Isra'ila ta ƙaɗdamar a Lebanon a Oktoban 2023 sun kashe fiye da mutum 2,350 da raba miliyan 1.2 da muhallansu.
Lebanon ta buƙaci MDD ta tilasta wa Isra'ila ta dakatar da kai hari ta kuma janye dakarunta
Lebanon ta buƙaci MDD ta tilasta wa Isra'ila ta dakatar da kai hari ta kuma janye dakarunta / Hoto: AP / AP
16 Oktoba 2024

Laraba, 16 ga Oktoban 2024

1241 GMT— Lebanon ta shigar da sabon ƙorafi ga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya domin tilasta wa Isra'ila dakatar da hare-haren da take kaiwa nan take tare da janye sojojinta daga yankin na Lebanon.

Sanarwar da Ma'aikatar Harkokin Wajen kasar ta fitar ta ce koken ya bukaci yin Allah wadai da "ci gaba da cin zarafi da Isra'ila ke yi kan kasar Labanon da kuma tilasta mata aiwatar da kuduri mai lamba 1701."

Ma'aikatar ta yi tir da "ci gaba da keta hurumin kasar Lebanon ta kai hari ta sama da ta ruwa da ta ƙasa, da Isra'ila ke yi, da kuma kai hari kan ofisoshin sojojin Lebanon da motocin daukar marasa lafiya da na agaji, da fararen hula… da kuma dirar wa ƙauyuka da birane."

Ta yi kira ga Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya yi Allah wadai da ci gaba da ci gaba da nuna kiyayyar da Isra'ila ke yi kan Lebanon da al'ummarta, da kuma mamayar da take yi a kasarta.

1221 GMT — Hare-haren Isra’ila sun kashe akalla shida kan gine-ginen kananan hukumomi a kudancin Lebanon

Ma'aikatar Lafiya ta kasar Lebanon ta sanar da cewa akalla mutum shida ne suka mutu sannan wasu 43 suka jikkata sakamakon harin da jiragen yakin Isra'ila suka kai kan wasu gine-ginen kananan hukumomin birnin Nabatie da ke kudancin kasar Lebanon.

Sanarwar da ma'aikatar ta fitar ta ce ana ci gaba da neman wadanda suka tsira da rayukansu a karkashin baraguzan ginin.

1210 GMT — Falasdinawa biyu sun mutu a harin da Isra’ila ta kai a Gaza

Akalla Falasdinawa biyu ne suka mutu yayin da wasu uku suka jikkata sakamakon wani hari da jiragen yakin Isra'ila suka kai kan wata mota a garin Al-Zawayda da ke tsakiyar Gaza, kamar yadda wata majiyar lafiya ta shaida wa Anadolu.

MAJIYA:TRT World
Rumbun Labarai
NATO na fuskantar ‘mummunar makoma’ idan ƙasashenta suka ƙi taimaka wa Amurka a yaƙin Iran - Trump
Trump ya ce bai shirya yin yarjejeniya ba domin kawo ƙarshen yaƙin Iran
Tsarin kiwon lafiya a Gabas ta Tsakiya na fuskantar barazana yayin da rikici ke ƙara muni: WHO
Kusan rabin rahotannin kafafen watsa labaran Birtaniya kan Musulmi na dauke da nuna wariya
Mashigar Hormuz: Hanyar ruwan da za ta iya girgiza tattalin arzikin duniya
Dalilai huɗu da suka sa matasan Afirka suka fi lafiyar ƙwaƙwalwa a duniya
Musulmai a Turkiyya, Oman, Singapore, da Australia za su fara azumin Ramadan a ranar Alhamis
'Babu wani takamaiman abin da aka cim ma' a ganawar Trump da Netanyahu a kan Iran
An ci tarar ƙananan hukumomi 10 a Holland kan binciken al'ummomin Musulmai ba tare da saninsu ba
Trevor Noah: Trump ya yi barazanar maka mai gabatarwa a Gasar Grammy a Kotu
Saudiyya da Isra'ila za su Amurka don tattaunawa yayin da Trump ke tura jiragen yaƙi na ruwa Iran
WHO: Amurka ta fita daga Hukumar Lafiya ta Duniya bayan shekara 78
Masana kimiyya sun gano zanen shacin hannu 'mai shekara 67,800' a wani kogo a Indonesia
Ministan Wajen Saudiyya da takwarorinsa na Iran, Oman da Qatar sun tattauna kan zaman lafiyar yanki
Amurka ta dakatar da ba da bizar masu ƙaura ga 'yan Nijeriya da wasu ƙasashe 74
Wani sanatan Amurka ya yi gargaɗi kan ƙaruwar ƙyamar Musulunci da ƙin jinin Larabawa
Trump ya saka harajin kashi 25 kan ƙasashen da ke kasuwanci da Iran
An katse intanet da wayoyin hannu a Iran
Matar shugaban Turkiyya ta gana da shugaban UNRWA kan shirin buɗe ofis a Ankara
Sanatocin Republican 5 sun bi sahun 'yan Democrat don neman sake duba ikon yaki na Trump a Venezuela