| hausa
AFIRKA
2 MINTI KARATU
Gwamnatin Katsina ta bayar da umarnin rufe makarantun koyon aikin lafiya masu zaman kansu
Gwamna Dikko Radda ya ɗauki matakin ne bayan wani bincike da Ma'aikatar Kiwon Lafiya ta gudanar da ya nuna makarantun ba su da inganci sannan da dama daga cikinsu ba su da rijista, lamarin da ya tayar da hankalin gwamnati.
Gwamnatin Katsina ta bayar da umarnin rufe makarantun koyon aikin lafiya masu zaman kansu
Gwamna Dikko Radda ya sha alwashin samar da kiwon lafiya mai inganci a jihar Katsina tun da ya hau kan mulki a 2023./Hoto:Gwamnatin Jihar Katsina
22 Oktoba 2024

Gwamnan Jihar Katsina da ke arewacin Nijeriya Dikko Radda ya bayar da umarnin rufe dukkan makarantun kowon kiwon lafiya masu zaman kansu da ke faɗin jihar tare da soke lasisinsu.

Mai bai wa gwamna shawara kan harkokin lafiya, Umar Mammada, ya sanar da wannan mataki ranar Litinin yayin tattaunawa da manema labarai a birnin Katsina.

Gwamnan ya ɗauki matakin ne bayan wani bincike da Ma'aikatar Kiwon Lafiya ta gudanar da ya nuna makarantun ba su da inganci sannan da dama daga cikinsu ba su da rijista, lamarin da ya tayar da hankalin gwamnati.

Mammada ya ce a shekarun baya-bayan, jihar ta Katsina ta samu ƙaruwar makarantun koyar da harkokin kiwon lafiya masu zaman kansu, waɗanda da dama daga cikinsu ba su da rajista kuma ba su da inganci.

“Ko da yake mun san muhimmiyar rawar da makarantun kiwon lafiya masu zaman kansu suke takawa wajen tabbatar da lafiyar al'umma, amma yana da muhimmanci mu tabbatar da ingancinsu domin kare lafiyar al'ummarmu," in ji Mammada.

Ya ƙara da cewa gwamnatin jihar za ta samar da tsari mai inganci da zai tabbatar da ƙwarewar irin waɗannan makarantu kafin a ba su damar ci gaba da horar da masu neman ilimin kiwon lafiya.

Jihar Katsina na cikin jihohin Nijeriya da ke fuskantar ƙalubale a fannin kiwon lafiya da tsaro kuma gwamnatin jihar ta sha alwashin shawo kan matsalolin, abin da ya sa masana suka yaba mata kan ɗaukar wannan mataki.

MAJIYA:TRT Afrika
Rumbun Labarai
MDD ta yi gargaɗi kan ƙazancewar yaƙin Sudan, ta yi kira kan barin shigar da kayan agaji
An gabatar da GH¢302bn a matsayin kasafin kuɗin Ghana na 2026 ga majalisar dokokin ƙasar
Sojojin Sudan sun daƙile harin RSF kan filin jirgin sama da dam a arewacin ƙasar
Rubio ya nemi a daina bai wa RSF makamai, ya ɗora wa rundunar laifi kan kashe-kashe a Al Fasher
Dalilin da ya sa TikTok ya goge bidiyoyi miliyan 1.5 da 'yan Uganda suka wallafa
Mutum 12 sun mutu a turmutsutsun neman aikin soja a Ghana – Rahotanni
Mahaucin Al Fasher: Yadda hotonsa ya zama alamar bakin cikin Sudan
UN Women: Mata da 'yan mata 11M suna fama da matsanancin ƙarancin abinci a Sudan sakamakon yaƙi
WHO ta bayyana damuwa kan karuwar masu ciwon siga a Afirka
Kisan kare dangi a boye da bayyane: Gushewar jinkai a Al Fasher
An ba da belin dan Gaddafi bayan da ya shafe shekaru 10 a tsare a Lebanon
Gwamnatin Trump 'ta aika wa Equatorial Guinea dala miliyan 7.5' don ta karɓi waɗanda Amurka ta kora
Ƙasashe fiye da 20 sun yi Allah wadai da RSF kan kashe-kashen da take yi a Sudan
Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya ya yi kira da a dakatar da zubar da jini a Sudan
Paul Biya na Kamaru: Dan siyasar da zai ci gaba da yin mulki har sai ya kai shekara 99?
Hare-haren RSF sun kori ƙarin dubban mutane daga Darfur da Kordofan na Sudan
RSF ta binne gawawwaki a kabarin bai-ɗaya, ta ƙone wasu domin 'ɓoye laifukan yaƙi': Likitocin Sudan
Sojojin Sudan sun harbo jirgi maras matuƙi na RSF a Kordofan ta Arewa
Dakarun Nijar sun cafke muggan makamai da aka yi safararsu daga Libya, sun kama masu safarar ƙwayoyi
RSF ta Sudan ta kai hare-hare a Jihar Khartoum da birnin Atbara bayan amincewa da tsagaita wuta