Shugaban Turkiyya Erdogan ya tattauna da shugaban Kongo Nguesso a gefen taron BRICS

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya gana da takwaransa na Kongo Denis Sassou Nguesso a gefen taron BRICS wanda aka gudanar a birnin Kazan na Rasha a ranar Alhamis.

By Mustapha Kaita
Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya tattauna da Shugaban Jamhuriyar Dimokuraɗiyar Kongo, Denis Sassou Nguesso a gefen taron BRICS. / Hoto: AA / Others

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya gana da takwaransa na Kongo Denis Sassou Nguesso a gefen taron BRICS wanda aka gudanar a birnin Kazan na Rasha a ranar Alhamis.

Tattaunawar ta kasance ta sirri a tsakanin shugabannin.

Ministan Makamashi da Albarkatu Alparslan Bayraktar da babban mai bai wa shugaban Turkiyya shawara kan tsare-tsaren ƙasashen waje da tsaro, Akif Cagatay Kilic na daga cikin waɗanda suka halarci tattaunawar.