| hausa
AFIRKA
2 MINTI KARATU
Ivory Coast ta ɗauke jakadanta da ma'aikatan diflomasiyanta daga Lebanon
Ma'aikatar harkokin wajen ƙasar ta Ivory Coast ta ce zuwa yanzu ƙasar ta kwashe kimanin mutum 100 daga Lebanon sakamakon ƙaruwar rikici, daga cikinsu har da ma'aikatanta na diflomasiya.
Ivory Coast ta ɗauke jakadanta da ma'aikatan diflomasiyanta daga Lebanon
Ivory Coast ta kwashe 'yan ƙasarta sakamakon ƙaruwar rikici tsakanin Hezbollah na Lebanon da Isra'ila. / Hoto: Reuters
27 Oktoba 2024

Ma'aikatar Harkokin Wajen Ivory Coast ta ce gwamnatin ƙasar a ranar Asabar ta fitar da jakadanta da jami'an diflomasiyya da kuma 'yan kasar da dama daga kasar Lebanon saboda karuwar rikici a yankin.

Ma'aikatar ta bayyana cewa ta kwashe kimanin mutum 100 ‘yan ƙasar ta Ivory Coast waɗanda kusan 60 daga cikinsu sun bayyana cewa suna so su bar ƙasar domin raɗin kansu.

Ma'aikatar ta ce ƙasar ta Ivory Coast ta shirya aikin kwashe ‘yan ƙasar daga Lebanon ne saboda tashin hankali tsakanin sojojin Isra'ila da mayakan Hezbollah.

Kusan mutum 20 sun bar ƙasar haka kuma za a ƙara kwasar ƙarin wasu idan aka samu gurbi a jiragen kasuwa, kamar yadda ma’aikatar harkokin wajen ƙasar ta ƙara da cewa.

Zuwa yanzu dai, sama da mutum 2,653 Isra’ilar ta kashe a Lebanon tun bayan soma wannan yaƙin.

MAJIYA:Reuters
Rumbun Labarai
Sojojin Sudan sun daƙile harin RSF kan filin jirgin sama da dam a arewacin ƙasar
Rubio ya nemi a daina bai wa RSF makamai, ya ɗora wa rundunar laifi kan kashe-kashe a Al Fasher
Dalilin da ya sa TikTok ya goge bidiyoyi miliyan 1.5 da 'yan Uganda suka wallafa
Mutum 12 sun mutu a turmutsutsun neman aikin soja a Ghana – Rahotanni
Mahaucin Al Fasher: Yadda hotonsa ya zama alamar bakin cikin Sudan
UN Women: Mata da 'yan mata 11M suna fama da matsanancin ƙarancin abinci a Sudan sakamakon yaƙi
WHO ta bayyana damuwa kan karuwar masu ciwon siga a Afirka
Kisan kare dangi a boye da bayyane: Gushewar jinkai a Al Fasher
An ba da belin dan Gaddafi bayan da ya shafe shekaru 10 a tsare a Lebanon
Gwamnatin Trump 'ta aika wa Equatorial Guinea dala miliyan 7.5' don ta karɓi waɗanda Amurka ta kora
Ƙasashe fiye da 20 sun yi Allah wadai da RSF kan kashe-kashen da take yi a Sudan
Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya ya yi kira da a dakatar da zubar da jini a Sudan
Paul Biya na Kamaru: Dan siyasar da zai ci gaba da yin mulki har sai ya kai shekara 99?
Hare-haren RSF sun kori ƙarin dubban mutane daga Darfur da Kordofan na Sudan
RSF ta binne gawawwaki a kabarin bai-ɗaya, ta ƙone wasu domin 'ɓoye laifukan yaƙi': Likitocin Sudan
Sojojin Sudan sun harbo jirgi maras matuƙi na RSF a Kordofan ta Arewa
Dakarun Nijar sun cafke muggan makamai da aka yi safararsu daga Libya, sun kama masu safarar ƙwayoyi
RSF ta Sudan ta kai hare-hare a Jihar Khartoum da birnin Atbara bayan amincewa da tsagaita wuta
Paul Biya na Kamaru: Shugaban da ya fi tsufa a duniya ya sha rantsuwar kama aiki karo na takwas
Hatsarin mota ya yi ajalin fiye da mutum 1,000 a Nijar a shekarar 2023, fiye da 12,000 sun jikkata