| Hausa
DUNIYA
4 MINTI KARATU
Jiragen saman Isra'ila sun kai hari Damascus a karo na biyu cikin kwana biyu
Yakin da Isra'ila ke yi a Gaza — wanda a yanzu ya shiga kwana na 406 — ya kashe akalla Falasdinawa 43,736 da jikkata 103,370, kuma ana fargabar 10,000 suna binne a ƙarƙashin ɓaraguzai. A Lebanon ma, Isra'ila ta kashe mutum 3,386 tun Oktoban bara.
Jiragen saman Isra'ila sun kai hari Damascus a karo na biyu cikin kwana biyu
Jiragen saman Isra'ila sun kai hari Damascus a karo na biyu cikin kwana biyu. / Hoto: Reuters / Photo: AP / AP

Juma'a, 15 ga Nuwamban 2024

1256 GMT —Kafafen yada labaran gwamnatin Syria sun ce Isra’ila ta kai hari a gundumar Mazzeh da ke Damascus, wanda shi ne hari na biyu cikin kwanaki da dama da aka kai a unguwar da ofisoshin jakadanci, hedkwatar tsaro da kuma ofisoshin Majalisar Dinkin Duniya ke da su.

Kamfanin dillancin labaran SANA ya bayyana cewa, Isra'ila ta hare-haren a yankin Mazzeh da ke Damascus," bayan rahoton da ya bayar da na wani mummunan harin da Isra'ila ta kai a gundumar kwana daya da ya gabata.

0320 GMT –– Isra'ila ta kai hari ginin hukumar kare farar hula a Lebanon, ta kashe mutum 12

Akalla mutum 12 ne suka mutu a ranar Alhamis a wani harin da Isra’ila ta kai ta sama inda ta lalata ginin hukumar tsaron farar hula a garin Douris da ke gundumar Baalbek a gabashin Lebanon.

Harin ta sama "ya faɗa garin Douris, wanda ya haifar da rugujewar ginin Hukumar Tsaro ta Farar Hula da kuma lalata ginin da ke kusa," in ji Kamfanin Dillancin Labarai na Labanon.

Adadin waɗanda aka bayar da rahoton sun rasu tun farko mutum bakwai ne. An gano gawawwakin waɗanda suka rasu sannan an aika da su wurin ajiyar gawawwaki a asibitin gwamnati na Baalbek. Kamar yadda kamfanin dillancin labaran ya ƙara da cewa.

0124 GMT —Jami'in Hamas ya ce ƙungiyar ta shirya tsagaita wuta ba tare da ɓata lokaci ba

Wani jigo a kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ya jaddada cewa a shirye suke don cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma sakin Isra'ilawan da aka yi garkuwa da su a matsayin wani bangare na musayar fursunoni "mai tsanani".

Basem Naim, wani likitan Falasdinu, ɗan siyasa kuma jigo a ofishin siyasa na Hamas, ya ce "yarjejeniya mai kyau da aka fayyace ta ƙarshe" ita ce ranar 2 ga Yuli.

"An tattauna dalla-dalla, kuma ina tsammanin muna kusa da tsagaita wuta… wanda zai iya kawo karshen wannan yakin, ya kawo tsagaita wuta na dindindin da janyewa baki daya da kuma musayar fursunoni," in ji shi a wata hira da Sky News.

Naim ya ce "Abin takaici, (Firaministan Isra'ila Benjamin) Netanyahu ya gwammace ya bi ta wata hanya" ya kuma tunatar da cewa "Isra'ila ta yi kisan kiyashi akalla biyu zuwa uku" a Khan Younis da kuma birnin Gaza bayan haka.

Dangane da kisan gillar da aka yi wa shugaban ofishin siyasa na Hamas Ismail Haniyeh a watan Yuli, ya ce tun bayan hakan, ba su sami "wata sahihiyar magana ba."

Karin bayani 👇

0003 GMT — Bam da aka harba daga Lebanon ya raunata sojojin Isra'ila 2

Sojojin Isra'ila biyu sun jikkata sakamakon fashewar wani jirgin mara matuki da aka harba daga kudancin Lebanon zuwa arewacin Isra'ila, a cewar rundunar.

Jaridar Yedioth Ahronoth ta bayar da rahoton cewa, jirgin mara matuki ya fado kuma ya fashe a sansanin Eliakim da ke kudancin Haifa bayan da sojojin tsaron saman Isra'ila suka fatattake su na kusan mintuna 40.

MAJIYA:TRT World
Rumbun Labarai
Faransa ta hana fita a sassan Paris yayin da zanga-zangar tsadar rayuwa ta haddasa tashin hankali
Trump ya ce Qatar ta yi tayin ba shi kyautar jirgin sama samfurin 747 bayan ya nemi a ba shi aro
Gwamnatin Trump na binciken Ilhan Omar, za ta ƙwace takardarta ta ‘yar ƙasa tare da korar ta: Rahoto
An cire wani sashe na huhun Fafaroma Leo bayan yi masa tiyatar kansa - Fadar Batikan
Koriya ta Arewa ta 'harba makamai masu linzami da dama cikin tekun Japan'
Trump ya ce rashin ba shi kyautar Nobel ta Zaman Lafiya 'abin kunya ne'
Faransa ta ce za ta bai wa Saudiyya kariya a ɓangaren man fetur ɗinta
HRW: Tasa ƙeyar ’yan Ci-rani zuwa Afirka da Amurka ke yi azabtarwa ce
Trump na shirin kai wa Iran hari kafin zaɓen tsakiyar wa'adi a Amurka - rahoto
WHO ta yi kira ga Rasha da ta yi gaskiya game da rahotannin mutuwa sakamakon annobar ciwon huhu
Amurka ta janye dukka jiragen yaƙinta na B-1 daga sansanin sojin saman Birtaniya saboda tsoron hari
Trump ya yi gargaɗin cewa yaƙi da Iran zai zo ƙarshe ko ta halin ƙaƙa 'nan ba da jimawa ba’
An ceto baƙin-haure 260 a gaɓar tekun Mauritania
Sau takwas sojojin Amurka na yunƙurin kashe kansu a cikin USS Abraham Lincoln, in ji gwamnatin Trump
Kwamitin Zaman Lafiya na Duniya zai gabatar da shirin farfado da Gaza na dala biliyan $2.45: Rahoto
Erdogan a UNGA: Gaza ce sansanin tsare mutane mafi muni da rashin tausayi da abin kunya a zamaninmu
Trump ya yi wa Iran barazana, ya kira ICC ‘marar gaskiya‘, ya sauya sunan AI zuwa ‘SI’
Amurka ta kai 'yan ci-rani fiye da 25,000 da ta kora zuwa ƙasashen da ba su da alaƙa da su: Bincike
Antonio Guterres ya nemi a bai wa Afirka kujerun dindindin a Kwamitin Tsaro na MDD
Trump ya sa hannu kan sabuwar dokar takunkumi ga Rasha: China da India na iya fuskantar sabon haraji