| hausa
AFIRKA
3 MINTI KARATU
An kashe sojojin Nijeriya biyar da 'yan Boko Haram da dama a wani hari a Borno
Wani hari da 'yan Boko Haram suka kai wani sansanin soja da ke jihar Borno a arewa maso gabashin Nijeriya ya yi sanadin mutuwar sojojin Nijeriya aƙalla biyar a ranar Talata, kamar yadda Hedkwatar Tsaro ta Ƙasar ta tabbatar.
An kashe sojojin Nijeriya biyar da 'yan Boko Haram da dama a wani hari a Borno
Sanarwar DHQ ta ƙara da cewa 'yan Boko Haram din sun kuma ƙona motar igwa ta sojoji da sauran wasu kayan yaƙin. / Hoto: Reuters
20 Nuwamba 2024

Aƙalla sojojin Nijeriya biyar ne suka mutu sakamakon wani harin ba-zata da 'yan ta'addar ƙungiyar Boko Haram suka kai a wani sansanin soji da ke ƙaramar hukumar Gubio a jihar Borno a arewa maso gabashin Nijeriya.

Hedkwatar Tsaron Nijeriya, DHQ a wata sanarwa a ranar Talata ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce sojojin waɗanda aka jibge ne don ba da kariya a yankin, kuma an kashe 'yan ta'addar ma da dama a arangamar.

"Harin wanda shiryayye ne ya yi sanadin mutuwar sojoji biyar da jikkata wasu 10, sai kuma huɗu da ba a gani ba har yanzu, sannan dakarun ma sun kawar da 'yan ta'addar da dama tare da ƙwato makamai," in ji daraktan watsa labarai na DHQ, Manjo Janar Edward Buba.

Mazauna yankin sun shaida wa kamfanin dillancin labaran Turkiyya na Anadolu cewa lamarin ya faru ne a ƙarshen mako a wani ƙauye, inda maharan suka jefa wa sansanin sojin bama-bamai daga ɓangarori daban-daban.

'Yan garin sun ce sun ji ƙarar harbe-harbe daga sansanin lokacin da sojojin suke musayar wuta da 'yan Boko Haram din, inda bayan awanni 'yan ta'addar suka sake kai harin har ma suka jikkata wasu fararen hula.

Sanarwar DHQ ta ƙara da cewa 'yan Boko Haram din sun kuma ƙona motar igwa ta sojoji da sauran wasu kayan yaƙin.

"Kazalika an tura wata tawagar sojin sama don karaɗe illahirin yankin da kuma gano hanyar da 'yan ta'addar ke bi," in ji Manjo Janar Buba.

Rundunar sojin ta ce yana da muhimmanci a fahimci cewa wannan harin ba zai kawar da hankalin dakaru da kuma rundunar sojin Nijeriya daga ƙoƙarin kawo ƙarshen ta'addanci da tayar da ƙayar baya da sauran matsalolin tsaro da ke addabar ƙasar ba.

Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya miƙa saƙon ta'aziyyarsa ga rundunar sojin ƙasar yana mai cewa wannan hari tunatarwa ce ga jihar kan irin rashin kan-gadon 'yan ta'addar Boko Haram.

MAJIYA:TRT Afrika
Rumbun Labarai
Sojojin Sudan sun daƙile harin RSF kan filin jirgin sama da dam a arewacin ƙasar
Rubio ya nemi a daina bai wa RSF makamai, ya ɗora wa rundunar laifi kan kashe-kashe a Al Fasher
Dalilin da ya sa TikTok ya goge bidiyoyi miliyan 1.5 da 'yan Uganda suka wallafa
Mutum 12 sun mutu a turmutsutsun neman aikin soja a Ghana – Rahotanni
Mahaucin Al Fasher: Yadda hotonsa ya zama alamar bakin cikin Sudan
UN Women: Mata da 'yan mata 11M suna fama da matsanancin ƙarancin abinci a Sudan sakamakon yaƙi
WHO ta bayyana damuwa kan karuwar masu ciwon siga a Afirka
Kisan kare dangi a boye da bayyane: Gushewar jinkai a Al Fasher
An ba da belin dan Gaddafi bayan da ya shafe shekaru 10 a tsare a Lebanon
Gwamnatin Trump 'ta aika wa Equatorial Guinea dala miliyan 7.5' don ta karɓi waɗanda Amurka ta kora
Ƙasashe fiye da 20 sun yi Allah wadai da RSF kan kashe-kashen da take yi a Sudan
Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya ya yi kira da a dakatar da zubar da jini a Sudan
Paul Biya na Kamaru: Dan siyasar da zai ci gaba da yin mulki har sai ya kai shekara 99?
Hare-haren RSF sun kori ƙarin dubban mutane daga Darfur da Kordofan na Sudan
RSF ta binne gawawwaki a kabarin bai-ɗaya, ta ƙone wasu domin 'ɓoye laifukan yaƙi': Likitocin Sudan
Sojojin Sudan sun harbo jirgi maras matuƙi na RSF a Kordofan ta Arewa
Dakarun Nijar sun cafke muggan makamai da aka yi safararsu daga Libya, sun kama masu safarar ƙwayoyi
RSF ta Sudan ta kai hare-hare a Jihar Khartoum da birnin Atbara bayan amincewa da tsagaita wuta
Paul Biya na Kamaru: Shugaban da ya fi tsufa a duniya ya sha rantsuwar kama aiki karo na takwas
Hatsarin mota ya yi ajalin fiye da mutum 1,000 a Nijar a shekarar 2023, fiye da 12,000 sun jikkata