Shekara 25 ta EAC: Kalubalen da Kungiyar Hadin Kan Kasashen Gabashin Afirka ke fuskanta
DUNIYA
6 MINTI KARATU
Shekara 25 ta EAC: Kalubalen da Kungiyar Hadin Kan Kasashen Gabashin Afirka ke fuskantaShekaru ashirin da biyar kenan bayan kafa ta, kungiyar yankin ta girma idan aka yi duba ga yawan mambobinta, amma kuma tana fama da matsalolin kare muradun kasa da na bai daya.
An marabci Somalia a kungiyar EAC -Photo- Ugandan President/X
27 Nuwamba 2024

Daga Edward Qorro

Kungiyar Hadin Kan Kasashen Gabashin Afirka mai mambobi takwas, wadda a ranar 30 ga Nuwamba za ta cika shekaru 30 da kafuwa, ta samo asali tun a 1967 a lokacin da Kenya da Uganda da Tanzania suka hada hannu waje guda don kafa EAC.

Manufar ita ce a habaka tattalin arziki da inganta kasuwancin yanki, da karfafa hadin kai a tsakanin kasashen Gabashin Afirka.

A yayin da kawancen ya rushe a 1977 saboda saɓani tsakanin mambobin, sake dawowar ƙawancen a 1999 na da matukar muhimmanci a tarihin hadin kai a nahiyar.

Amma duk da wannan ci gaba da aka samu, bikin cika shekara na 25 EAC ya zama kamar na kallon baya da kuma me aka aikata, maimakon bikin murna.

Batutuwa irin su cire haraji da karanci kasuwanci a tsakaninsu na ci gaba da addabar kawancen kasashen takwas - Jumhuriyar Dimokuradiyyar Kongo da Burundi da Kenya da Rwanda da Sudan ta Kudu da Uganda da Tanzania - saboda bukatun kowa na musamman na zuwa gaba da bukatun bai daya na yankin.

"A wasu lokutan, wadannan matsaloli na zuwa ne daga bangaren 'yan kasuwa da ke ta roƙo saboda kayayyakinsu da suke sayarwa da ba sa so a zo a yi gogayya da su daga sauran kasashe mambobin EAC," kamar yadda Shugaban riƙo na Kungiyar 'Yan Kauswar Gabashin Afirka, Adrian Njau ya fada wa TRT Afrika.

Ya bayyana bukatar da ke akwai ta bangaren masu zaman kansu da rage tsadar gudanar da kasuwanci a yankin, maimakon batun janye haraji.

Kalubale ga kasuwanci, wani rahoton EAC da aka fitar a 2023 ya bayyana cewa tun 2007 aka cire shingen biyan haraji, amma aƙalla akwai bangarori 10 da ake ci gaba da taƙaddama a kansu.

Wadannan shingaye na haraji na nufin wasu ƙa'idoji na fito masu wahalarwa da ke nuna bambancin wajen aiwatar da doka.

Njau ya ɗora alhakin hakan a kawunansu kan samar da yanayi mara kyau da kawo tsare-tsare marasa tasiri da rage jin dadin kwastomomi, da hana kasuwanci tsakanin mambobin EAC.

"Dokokin kan iyaka marasa tasiri na ƙara ta'azzara lamarin. Duk da cewa abubuwa irin su batun janye haraji da jan kafa wajen warware al'amura, da rashin gaskiya na ƙara hana cigaba," ya bayyana haka.

A EABC, da ke da hedkwata a garin Arusha na Tanzania, babbar damuwarta ita ce yadda harajin ke ci gaba har bayan da aka ce an janye su.

Wannan ne ya sanya majalisar 'yan kasuwar yankin ke kira da a dauki ƙwararan matakan kawar da kalubalen.

A yayin da EAC ke shirin bikin shekara 25 da kafa ta, har yanzu batun samar da kudin bai daya a tsakanin kasashen EAC ba ya kan gaba, inda aka mayar da wannan manufa zuwa shekarar 2031.

Kungiyar Kula da Kudade, ginshiƙi na uku na neman hadewar EAC, an sa ran kafa ta a 2024, inda za ta samar da kudin bai daya da samar babban banki na yanki.

Shirin Kafa Hukumar Kudin ya hada da samar da tsarin dunkule manyan harkokin kudi da kafa hukumomi don tallafa wa aiwatar da ƙa'idoji, da hadewar manufofi da tsare-tsare.

Shugaban Kungiyar EABC na da fata mai kyau na cewar wannan shiri zai amfanar.

"Manufar samar da kudin bai daya nan da shekarar 2031 kawai buri ne amma zai iya tabbata, matukar dai kasashe mambobi sun yi yadda ya dace na cika burin dunkulewarsu waje guda." Njau ya fada wa TRT Afrika.

Daga cikin manyan sharuddan samar da kudin bai daya ga EAC har da ƙaƙƙarfar hadewar hada-hadar tattalin arziki, kamar tsayar da tashin farashin kayayyaki kan kashi takwas kawai, kawar da gibin kudade na kashi uku, da kayyade bashi da kashi hamsin bisa ka'idojin yau.

Njau na kallon mafi yawan mambobin EAC da suna kan turba duk da kalubalen da ake fuskanta wajen cim ma sharuɗan bashi da kudaden da ake samu idan aka kwatanta da gibin kasafin kudi, wanda bukatar muhimman ayyuka ke janyo wa, tare da kashe kudade don rage radadi da tasirin tattalin arziki.

Wasu karin matsalolin su ne nauyin biyan basussukan kasashen waje da kasuwancin duniya da ke fuskantar cikas.

Dukkan manyan bankunan kasashen EAC sun amince da su sauya manufofin kudadensu daga na ajiye kudaden rara zuwa na tabbatar da darajar kudaden ta daga.

"Mun yi amanna cewa karin wa'adi na bayar da damar kawar da wadannan matsaloli."

"Ana bukatar kokari mai ɗorewa don gina tsare-tsaren hukumomi da dokoki don samar da kudin bai daya," in ji Njau.

Game da kasuwanci a tsakanin kasashen EAC kuma, ya ƙaru a cikin 'yan shekarun nan, saboda tsare-tsare sabbi da aka kawo irin su Mahukuntan Fito na Bai Daya da Matakan kasuwanci su ma na bai daya, da zuba jari wajen samar da kayan more rayuwa.

Sai dai kuma, duk wadannan matakan na ƙasa da yadda aka tsammata, inda kasuwancin da ke tsakaninsu yake bisa kashi 15 kawai.

Kasuwanci tsakanin kasashen ya haɓaka da kashi 13.1 a 2023, inda ya kai na dalar Amurka biliyan 12.1.

"Domin habaka kasuwancin yankin, dole ne kasashe mambobin EAC su aiwatar da yarjeniyoyin da aka kulla," in ji Njau.

MAJIYA:TRT Afrika
Rumbun Labarai
Rasha ta ce tana sa ido kan Nijeriya bayan barazanar da Trump ya yi ta kai hari kasar
Zohran Mamdani: Matashi Musulmi na farko ya lashe zaɓen Magajin Birnin New York
Yadda amfani da magungunan antibiotic barkatai ya sa cututtuka suka zama makamai
Rundunar Sojin Ruwan Pakistan ta kama mugwayen ƙwayoyi na dala biliyan ɗaya a Tekun Arebiya
An gano sauro a karon farko a ƙasar Iceland
Yadda hukumomi a India suke farautar Musulmai da suke cewa 'Ina son Annabi Muhammad'
Putin ya gargaɗi Trump cewa bai wa Ukraine makamai mai linzamin Tomahawk zai jawo matsala tsakaninsu
Abin da muka sani game da mummunar arangamar kan iyaka tsakanin sojin Pakistan da Afganistan
Waiwayen 1903: An taɓa yi wa Yahudawa tayin Afirka, kamar yadda ake so a mayar da Falasɗinawa yanzu
An naɗa Sarah Mullally mace ta farko Shugabar Cocin Ingila
Yadda mutuwar ɓauna a turmutsutsu ke sauya salon farautar manyan namun dawa
An tsinci gawar jakadan Afirka ta Kudu a Faransa a wajen otal a birnin Paris
Babban Alkalin Kotun Amurka ya dakatar da umarnin Trump na korar ma’aikatan VOA
UNGA: Yadda ta kaya a taron 'nuna wa juna yatsa da huce haushi' na Majalisar Dinkin Duniya
Yadda jami'an diflomasiyyar duniya suka fice daga Zauren UNGA yayin da Netanyahu zai yi jawabi
Jawabin Trump a taron MDD ya fito da sakamakon nuna ƙyamar Musulunci a duniya
An yanke wa tsohon Shugaban Faransa Sarkozy hukuncin shekara biyar a gidan yari
UNGA 80: Trump ya yi alkawarin hana Isra'ila shirin ƙwace Yammacin Kogin Jordan
Ga manyan batutuwa huɗu daga jawabin Sarkin Qatar a taron UNGA
Muradun Ƙungiyar G7 a UNGA sun haɗa da ƙara tallafa wa Ukraine da neman tsagaita wuta a Gaza