| hausa
AFIRKA
2 MINTI KARATU
Gwamnatin Nijar ta dakatar da watsa shirye-shiryen BBC a ƙasar
Wata sanarwa da Ministan Watsa Labaran Jamhuriyar Nijar, Sidi Mohamed Raliou ya fitar ta ce an dakatar da watsa duka shirye-shiryen BBC kai-tsaye da na abokan hulɗarta na ƙasar da suka haɗa da R&M da Saraounia da Anfani har tsawon wata uku.
Gwamnatin Nijar ta dakatar da watsa shirye-shiryen BBC a ƙasar
A makon nan ne dai BBC ta bayar da rahoton cewa ƙungiyoyin masu tayar da kayar baya sun kashe dakarun sojin Nijar 90 a fafatawar da suka yi, rahoton da gwamnatin ƙasar ta musanta. . / Hoto: AFP
13 Disamba 2024

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta dakatar da watsa shirye-shiryen kafar watsa labarai ta BBC a ƙasar har tsawon wata uku.

Wata sanarwa da ta fito daga ofishin Ministan Watsa Labarai na Jamhuriyar Nijar, Sidi Mohamed Raliou, ta ce an dakatar da watsa duka shirye-shiryen BBC kai-tsaye da na abokan hulɗarta na ƙasar da suka haɗa da R&M da Saraounia da Anfani har tsawon wata uku.

Gwamnati ta ce an ɗauki matakin ne saboda yadda kafar ta BBC ta watsa bayanan 'ƙarya' waɗanda za su iya kawo matsala ga kwanciyar hankali a ƙasar, da kuma dakushe karsashin dakarun ƙasar.

A makon nan ne dai BBC ta bayar da rahoton cewa ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya sun kashe dakarun sojin Nijar 90 a fafatawar da suka yi, rahoton da gwamnatin ƙasar ta musanta.

Kazalika gwamnatin ta Nijar ta ce za ta gurfanar da gidan rediyon Faransa (RFI) a gaban kotu bayan ta zarge shu da neman haddasa fitina tsakanin al'umma da “zummar haifar da kisan ƙare-dangi.”

Sai dai a ranar Larabar da ta gabata Rundunar Sojin Nijar ta musanta harin, inda ta bayyana rahotannin wannan ta'asa a matsayin "kalmomi mara tushe".

Tsawon shekaru Nijar -- tare da makwabtanta biyu Burkina Faso da Mali -- na fama da tashe-tashen hankula na masu iƙirarin jihadi.

A kwanakin baya ƙasashen sun kafa ƙungiyar Sahel Alliance wadda ta shafi inganta tattalin arziki da tsaron ƙasashen.

MAJIYA:TRT Afrika
Rumbun Labarai
An ba da belin dan Gaddafi bayan da ya shafe shekaru 10 a tsare a Lebanon
Gwamnatin Trump 'ta aika wa Equatorial Guinea dala miliyan 7.5' don ta karɓi waɗanda Amurka ta kora
Ƙasashe fiye da 20 sun yi Allah wadai da RSF kan kashe-kashen da take yi a Sudan
Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya ya yi kira da a dakatar da zubar da jini a Sudan
Paul Biya na Kamaru: Dan siyasar da zai ci gaba da yin mulki har sai ya kai shekara 99?
Hare-haren RSF sun kori ƙarin dubban mutane daga Darfur da Kordofan na Sudan
RSF ta binne gawawwaki a kabarin bai-ɗaya, ta ƙone wasu domin 'ɓoye laifukan yaƙi': Likitocin Sudan
Sojojin Sudan sun harbo jirgi maras matuƙi na RSF a Kordofan ta Arewa
Dakarun Nijar sun cafke muggan makamai da aka yi safararsu daga Libya, sun kama masu safarar ƙwayoyi
RSF ta Sudan ta kai hare-hare a Jihar Khartoum da birnin Atbara bayan amincewa da tsagaita wuta
Paul Biya na Kamaru: Shugaban da ya fi tsufa a duniya ya sha rantsuwar kama aiki karo na takwas
Hatsarin mota ya yi ajalin fiye da mutum 1,000 a Nijar a shekarar 2023, fiye da 12,000 sun jikkata
Sabbin hotunan tauraron dan'adam sun gano alamun 'kaburburan bai-daya a El-Fasher a Sudan
MDD ta yi gargaɗin cewa yaƙin Sudan na gurgunta tattalin arzikin Sudan ta Kudu
Trump ya ce bai kamata Afirka ta Kudu ta kasance cikin G20 ba, ba zai je taronta a Johannesburg ba
'Yan Sudan sun ba da mummunan labarin yi wa mata fyade yayin da suke tserewa daga Al Fasher
An kashe mutane 40 a harin da aka kai wa taron jana'iza a yankin Kordofan na Sudan: MDD
Yadda biranen Afirka mafiya tsafta suke bayyana sauyin da ake samu a nahiyar
Sojojin Ruwa na Ghana sun kama ‘yan Nijeriya 10 da suka ɓuya a jirgin ruwan Panama a Tema
Harin jirgin sama maras matuƙi na RSF ya kashe mutane da dama a lardin Kordofan na Arewa a Sudan