Erdogan ya buƙaci Italiya da ta jagoranci yunƙurin dage takunkumin da aka sa wa Syria

Shugaba Erdogan ya jaddada gaggawar sake gina kasar Siriya a ziyarar da ya yi da firaministan Italiya.

By Halima Umar Saleh
Shugaba Erdogan ya jaddada gaggawar sake gina kasar Siriya a ziyarar da ya yi da firaministan Italiya. / Hoto: AA Archive / Others

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya jaddada bukatar daukar matakin gaggawa don tallafa wa yunkurin sake gina kasar Siriya a lokacin da ya tattauna da firaministan Italiya Giorgia Meloni ta wayar tarho.

Shugabannin sun tattauna kan rikicin da ke faruwa a kasar Siriya, inda Erdogan ya bayyana alfanun da ke tattare da dage takunkumin da aka kakaba wa kasar, ya kuma bukaci Italiya da ta taka rawar gani a wannan mataki.

Shugabannin biyu sun mayar da hankali ne kan karfafa alakar da ke tsakanin kasashen biyu da magance muhimman batutuwan da suka shafi shiyya-shiyya da na duniya baki daya.

A yayin tattaunawar, Erdogan ya yi karin haske kan dangantakar kasuwanci tsakanin Turkiyya da Italiya, inda ya ce kasashen biyu sun samu karfin cinikin dala biliyan 32 a shekarar 2024.

Ya bayyana fatansa game da kara inganta wannan adadi ta hanyar fadada ciniki da zuba jari, musamman a fannonin tsaro da makamashi.

Tattaunawar ta sake jaddada aniyar kasashen biyu na zurfafa hadin gwiwa a fannoni daban daban da kuma tinkarar kalubalen da ke fuskantar duniya baki daya.