| Hausa
AFIRKA
3 MINTI KARATU
'Yan bindiga sun kashe sojoji 30 a Jamhuriyar Benin
Wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka kai harin ga sojojin a garin Banikoara da ke arewacin Jamhuriyar Benin.
'Yan bindiga sun kashe sojoji 30 a Jamhuriyar Benin
Wannan shi ne harin ta'addanci mafi muni da aka kai a kasar dangane da asarar rayukan mutane a 'yan kwanakin nan, in ji kafar yada labaran kasar. / Hoto: Ministère de la Défense Nationale / Others
10 Janairu 2025

Akalla sojojin kasar Benin 30 ne aka kashe a garin Banikoara da ke arewacin kasar a lokacin da wasu da ba a san ko su waye ba suka kai musu hari, kamar yadda wani jami’in sojin kasar ya bayyaba a yammacin Alhamis.

Rahotannin farko da kafafen watsa labarai suka fara ruwaitowa sun ce an kashe sojoji 28 a harin ta’addancin da aka kai ranar Laraba a Banikoara, da ke kan iyaka tsakanin Benin, Burkina Faso da Nijar.

Sai dai wani jami’in sojan kasar ta Benin da ya bukaci a sakaya sunansa ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu ta wayar tarho cewa aƙalla sojoji 30 ne suka mutu a harin, kuma sojoji sun kaddamar da farmaki kan ‘yan ta’addan da ke yankin, wanda hakan ya sa aka ci galaba sosai a kan ‘yan ta’adan.

Sai dai jami’in ya ce a halin yanzu ana ci gaba da tattara bayanan hukuma kuma nan ba da jimawa ba za a fitar da sanarwa ga manema labarai domin bayar da karin bayani game da harin da kuma farmakin da sojojin suka kai.

A ranar Alhamis din da ta gabata ne kafar yada labaran kasar Olofofo ta ruwaito cewa an kwashe kusan sa’o’i takwas ana musayar wuta sannan kuma maharan sun kashe tare da kona sojojin Benin 30.

Wannan shi ne harin ta'addanci mafi muni da aka kai a kasar dangane da asarar rayukan mutane a 'yan kwanakin nan, in ji kafar yada labaran kasar.

Rundunar sojojin kasar ta Benin ba ta bayyana kungiyar ta'addancin da ta kai harin ba.

Sai dai hare-haren da ake kaiwa arewacin Benin ya karu a shekarun baya-bayan nan, musamman na kungiyar ISIS (Daesh) da kungiyoyin ta'addancin al-Qaeda da ke aiki a kasashe makwabta. Yankin kan iyaka da Burkina Faso ya kasance cibiyar hare-haren.

MAJIYA:AA
Rumbun Labarai
Sudan: Aƙalla mutum 21 sun mutu a hatsarin kwale-kwale a Kogin Nilu
Kasashe shida sun shiga Kwamitin Tsaro na Tarayyar Afirka
RSF ta kashe ƙananan yara a harin da ta kai wani masallaci a yankin Kordofan na Sudan
Saudiyya ta yi tur da RSF kan munanan ayyukanta a Al Fasher, ta buƙaci a ba da hanyar kai agaji
Mutum biyar sun mutu a hatsarin helikwaftan ɗaukar marasa lafiya a Libya
Yadda 'yan Somaliya suka gina wa tsohon shugaba ƙasarsu Farmaajo sabon gida
Sake dawo da ainihin martabar Afirka
RSF ta Sudan ta kai hari da jirgi maras matuƙi, ta kashe gomman mutane da yara
Dubban ‘yan kasar Libya sun taru don halartar jana'izar Saif al-Islam Gaddafi
Harin RSF a wani asibiti a Sudan ya kashe mutum 22, ciki har da ma'aikatan jinya
Ghana da Zambia sun ƙulla yarjejeniyar shiga ƙasashen juna ba tare da biza ba yayin ziyarar Mahama
Saif al-Islam Gaddafi: An kashe ɗan marigayi shugaban Libya Muammar Gaddafi
Afirka na fuskantar tarnaƙin bashin dala biliyan 90 a 2026, in ji S&P
Yadda Biteye na Senegal ke amfani da ƙwallon ƙafa don samun waraka ga ƙwaƙwalwa
Sojojin Rasha sun taimaka wajen daƙile hari a filin jirgin saman Nijar: Moscow
'Yanbindiga sun kashe sojojin Libya uku a kusa da kan iyakar Nijar
Sudan ta sake buɗe filin jiragen sama na Khartoum bayan yaƙin kusan shekaru uku
Nijar: Ƙungiyar Daesh ta ɗauki nauyin harin da aka kai sansanin sojin sama na Yamai
Fiye da mutum 200 sun rasu bayan ruftawar wurin haƙar coltan a Jamhuriyar Kongo
Ƙungiyar Tarayyar Afirka ta sha alwashin goyon bayan Nijar bayan kai hari a filin jirgin saman Yamai