An kashe sojojin Isra'ila 10 cikin kwana uku a arewacin Gaza — Hamas

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta ce mayakanta sun kashe sojojin Isra'ila 10 a arewacin Gaza a cikin kwanaki ukun da suka gabata.

By Halima Umar Saleh
Babu wani martani har yanzu daga ɓangaren Isra'ila. / Hoto: Reuters / Reuters

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta ce mayakanta sun kashe sojojin Isra'ila 10 a arewacin Gaza a cikin kwanaki ukun da suka gabata.

"Sama da sojojin Isra'ila 10 aka kashe tare da jikkata wasu da dama a hare-haren da 'yan adawa suka kai a cikin sa'o'i 72 da suka gabata," in ji Abu Obaida, kakakin reshen kungiyar Hamas, na kungiyar Qassam Brigades, kamar yadda ya bayyana a cikin wata sanarwa.

Ya ce asarar da sojojin Isra'ila suka yi "ta fi yadda aka sanar." Ya ci gaba da cewa: "Za a yi galaba kan makiya (Isra'ila) daga arewacin Gaza, kuma za su ga wulakanci ba tare da samun damar karya tirjiya ba."

Kakakin ya ce nasarorin da sojojin Isra'ila suka samu a arewacin Gaza su ne "lalata abubuwa da ɓarna da kisan kiyashi kan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba."

Babu wani martani har yanzu daga ɓangaren Isra'ila.