Neymar ya miƙa saƙon ban-kwana bayan barin Al-Hilal
A wannan makon ne Al-Hilal ta soke kwantiraginsa duk da yana da sauran watanni shida, bayan gazawarsa ta buga musu wasanni sakamakon yawan tafiya doguwar jinya da ya yi ta yi.
Mashahurin ɗan wasa kuma tsohon kyaftin ɗin tawagar ƙasar Brazil, Neymar, ya miƙa saƙon ban-kwana ga masoya ƙungiyar Al Hilal ta Saudiyya, bayan da zamansa a ƙungiyar ya zo ƙarshe.
Ɗan wasan zai koma tsohuwar ƙungiyarsa da ke Brazil, wato Santos, wadda a can ne ya fara buga ƙwallo tun yana matashi, kafin ya koma Barcelona a 2013.
Al wannan makon ne Al-Hilal ta soke kwantiraginsa duk da yana da sauran watanni shida, bayan gazawarsa ta buga musu wasanni sakamakon yawan tafiya doguwar jinya da ya yi ta yi.
A baya an yi ta raɗe-raɗin cewa Neymar zai koma Santos, musamman ganin yadda Al-Hilal ta cire sunansa daga jerin 'yan wasan da za su buga mata ragowar wasannin kakar bana.
Neymar ya wallafa saƙo a Instagram, inda yake cewa, "Ga kowa a Al Hilal, ga masoya, Na gode!! Na ba da duka ƙarfina don ganin na buga wasa kuma na yi fatan a ce zamana a can ya fi haka kyau."
Zaftarewar albashi
Gabanin zuwansa Saudiyya, Neymar wanda ke da shekarunsa 32 a yanzu, ya buga wa manyan ƙungiyoyi kamar Barcelona da PSG, amma a Al-Hilal jinya ta hana shi sukunin buga wasanni.
A bazarar 2023 ne Neymar ya bar Paris Saint-Germain zuwa Al-Hilal kan kuɗin da ya kai a dala miliyan $98, amma sau bakwai kacal ya buga musu wasa a duka gasanni.
Ana kallon wannan kwantiragi a matsayin mafi asara a tarihin cinikin 'yan wasan ƙwallo.
A yanzu dai rahotanni na cewa Neymar ya haƙura da a zaftare albashinsa a Santos, inda zai koma dindindin, maimakon tafiya aro.