| Hausa
DUNIYA
3 MINTI KARATU
Erdogan: Babu wani mai ƙarfin iko da ya isa ya tilasta wa Falasɗinawa barin ƙasarsu
"Babu wani mutum da yake da ikon fitar da mutanen Gaza daga ƙasarsu, wadda aka kafa dubban shekaru. Yankin Falasɗinu, wanda ya haɗa da Gaza, Gaɓar Yammacin Kogin Jordan da Gabashin Birnin Ƙudu, na Falasɗinawa ne,"  in ji Recep Tayyip Erdogan.
Erdogan: Babu wani mai ƙarfin iko da ya isa ya tilasta wa Falasɗinawa barin ƙasarsu
Erdogan ya jinjina wa ƙungiyar Hamas bisa cika alƙawuran da ta ɗauka na yin musayar fursunoni da Isra'ila, duk kuwa da cewa ta yi ƙoƙarin keta yarjejeniyar. . / Hoto: AA / Others
10 Fabrairu 2025

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya jaddada cewa babu wani mai ƙarfin iko da ya isa ya tilasta wa mutanen Gaza ficewa daga ƙasarsu ta “dindindin”, domin kuwa yankin Gaza da Gaɓar Yammacin Kogin Jordan da Gabashin Birnin Ƙudus yankuna ne mallakin Falasɗinawa.

"Babu wani mutum da yake da ikon fitar da mutanen Gaza daga ƙasarsu, wadda aka kafa dubban shekaru. Yankin Falasɗinu, wanda ya haɗa da Gaza, Gaɓar Yammacin Kogin Jordan da Gabashin Birnin Ƙudu, na Falasɗinawa ne," in ji Recep Tayyip Erdogan a hira da manema labarai ranar Lahad a Istanbul kafin ya tashi zuwa ƙasar Malaysia.

Shawarar da shugaban Amurka Donald Trump ya bayar game da da kwashe Falasɗinawa daga yankin Gaza, bayan shan matsin lamba daga Yahudawa masu tsaurin ra'ayi, ba batu ne da ya kamata a tattauna a kansa ba, in ji Shugaba Erdogan.

Kazalika Erdogan ya jinjina wa ƙungiyar Hamas bisa cika alƙawuran da ta ɗauka na yin musayar fursunoni da Isra'ila, duk kuwa da cewa ta yi ƙoƙarin keta yarjejeniyar.

Game da halin da ake ciki a Syria, Shugaba Erdogan ya ce ana ci gaba da tono manyan ƙaburbura a sassa daban-daban na Syria, lamarin da ke ƙara tona asirin gwamnatin Assad.

Shugaban Turkiyya ya bayyana fatansa na ganin an samu zaman lafiya a Syria a ƙarƙashin jagorancin Shugaba Ahmed Alsharaa, yana mai cewa nan ba da jimawa ba ƙasar za ta samu kwanciyar hankali.

Babu gurbin ƙungiyoyin 'yan ta'adda a Syria, in ji Erdogan, wanda ya jaddada cewa shugaban Syria Ahmad Alsharaa zai yi yaƙi da waɗannan ƙunguyoyi.

MAJIYA:TRT World
Rumbun Labarai
Chadi za ta tura sojoji 750 domin yaƙar 'yandaban Haiti
Trump: Amurka na duba yiwuwar 'kammala' hare-haren soji kan Iran
NATO na fuskantar ‘mummunar makoma’ idan ƙasashenta suka ƙi taimaka wa Amurka a yaƙin Iran - Trump
Trump ya ce bai shirya yin yarjejeniya ba domin kawo ƙarshen yaƙin Iran
Tsarin kiwon lafiya a Gabas ta Tsakiya na fuskantar barazana yayin da rikici ke ƙara muni: WHO
Kusan rabin rahotannin kafafen watsa labaran Birtaniya kan Musulmi na dauke da nuna wariya
Mashigar Hormuz: Hanyar ruwan da za ta iya girgiza tattalin arzikin duniya
Dalilai huɗu da suka sa matasan Afirka suka fi lafiyar ƙwaƙwalwa a duniya
Musulmai a Turkiyya, Oman, Singapore, da Australia za su fara azumin Ramadan a ranar Alhamis
'Babu wani takamaiman abin da aka cim ma' a ganawar Trump da Netanyahu a kan Iran
An ci tarar ƙananan hukumomi 10 a Holland kan binciken al'ummomin Musulmai ba tare da saninsu ba
Trevor Noah: Trump ya yi barazanar maka mai gabatarwa a Gasar Grammy a Kotu
Saudiyya da Isra'ila za su Amurka don tattaunawa yayin da Trump ke tura jiragen yaƙi na ruwa Iran
WHO: Amurka ta fita daga Hukumar Lafiya ta Duniya bayan shekara 78
Masana kimiyya sun gano zanen shacin hannu 'mai shekara 67,800' a wani kogo a Indonesia
Ministan Wajen Saudiyya da takwarorinsa na Iran, Oman da Qatar sun tattauna kan zaman lafiyar yanki
Amurka ta dakatar da ba da bizar masu ƙaura ga 'yan Nijeriya da wasu ƙasashe 74
Wani sanatan Amurka ya yi gargaɗi kan ƙaruwar ƙyamar Musulunci da ƙin jinin Larabawa
Trump ya saka harajin kashi 25 kan ƙasashen da ke kasuwanci da Iran
An katse intanet da wayoyin hannu a Iran