| hausa
AFIRKA
2 MINTI KARATU
ECOWAS na neman taimakon Turkiyya domin daƙile matsalolin tsaronta
A cikin shekarun nana, Turkiyya da kuma ƙasashen Afirka da dama sun zurfafa dangantaka ta tsaro da tattalin arziƙi da al'adu a tsakanin su.
ECOWAS na neman taimakon Turkiyya domin daƙile matsalolin tsaronta
Yankin Yammacin Afirka da ke ƙarƙashin ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasasshen Afirka ta Yamma ( ECOWAS) na fama da matsaloli na 'yan ta'adda da ɓarayin daji. / Hoto: Reuters
12 Fabrairu 2025

Ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen yammacin Afirka, ECOWAS ta yi kira ga Turkiyya ta ƙara tallafi ga ƙasashen da ke yankin a ƙoƙarin su na daƙile matsaloli n atsaro.

Shugaban hukumar ƙungiyar ta ECOWAS , Omar Touray, ya yi wannan kiran ne a lokacin da jakadan Turkiyya a Nijeriya mai barin gado, Hidayet Bayraktar, ya kai masa ziyarar bankwana ranar Talata, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Nijeriya ya ruwaito.

Touray ya yaba wa rawan da Turkiyya ke takawa a Afirka da kuma duniya , yana mai kira gareta da ta ci gaba da taiamakawa wajen yaƙi da ƙungiyoyin 'yan ta'dda da kuma tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Yammacin Afirka.

"Turkiyya babbar ƙawar hulɗa ce a Afirka kuma ƙawar hulɗa mai gata ce ga ECOWAS. Ana yaba wa shugabancin ta tare da gamsuwa da ita a faɗin nahiyar Afirka," in ji Touray.

"Ƙalubalen da ECOWAS ta fi fama da shi ne rashin tsaro, kuma babu ɗaya daga cikin mabobinta da za ta iya fuskantar sa ita kaɗai ," a cewarsa.

A nasa ɓangaren, jakadan Turkiyya mai barin gado, Hidayet Bayraktar, ya nanata jajircewar Turkiyya wajen zurfafa tallafinta magance matsalolin masu tsattsauran ra'ayi da kuma ta'addanci tare da inganta zaman lafiya da tsaro a yankin.

Turkiyya da ƙasashen Afirka sun ƙarfafa hulɗarsu ta soji da tattalin arziƙi da kuma al'adu yayin da Ankara take sake zama zaɓi a maimakon ƙasashen yamma masu ƙarfin tattalin arziƙi.

Wasu ƙasashen Afirka sun sayi kayayyakin soji ciki har da jirage mara matuƙa daga Turkiyya domin inganta ƙarfin sojinsu.

MAJIYA:TRT Afrika da abokan hulda
Rumbun Labarai
Sojojin Sudan sun daƙile harin RSF kan filin jirgin sama da dam a arewacin ƙasar
Rubio ya nemi a daina bai wa RSF makamai, ya ɗora wa rundunar laifi kan kashe-kashe a Al Fasher
Dalilin da ya sa TikTok ya goge bidiyoyi miliyan 1.5 da 'yan Uganda suka wallafa
Mutum 12 sun mutu a turmutsutsun neman aikin soja a Ghana – Rahotanni
Mahaucin Al Fasher: Yadda hotonsa ya zama alamar bakin cikin Sudan
UN Women: Mata da 'yan mata 11M suna fama da matsanancin ƙarancin abinci a Sudan sakamakon yaƙi
WHO ta bayyana damuwa kan karuwar masu ciwon siga a Afirka
Kisan kare dangi a boye da bayyane: Gushewar jinkai a Al Fasher
An ba da belin dan Gaddafi bayan da ya shafe shekaru 10 a tsare a Lebanon
Gwamnatin Trump 'ta aika wa Equatorial Guinea dala miliyan 7.5' don ta karɓi waɗanda Amurka ta kora
Ƙasashe fiye da 20 sun yi Allah wadai da RSF kan kashe-kashen da take yi a Sudan
Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya ya yi kira da a dakatar da zubar da jini a Sudan
Paul Biya na Kamaru: Dan siyasar da zai ci gaba da yin mulki har sai ya kai shekara 99?
Hare-haren RSF sun kori ƙarin dubban mutane daga Darfur da Kordofan na Sudan
RSF ta binne gawawwaki a kabarin bai-ɗaya, ta ƙone wasu domin 'ɓoye laifukan yaƙi': Likitocin Sudan
Sojojin Sudan sun harbo jirgi maras matuƙi na RSF a Kordofan ta Arewa
Dakarun Nijar sun cafke muggan makamai da aka yi safararsu daga Libya, sun kama masu safarar ƙwayoyi
RSF ta Sudan ta kai hare-hare a Jihar Khartoum da birnin Atbara bayan amincewa da tsagaita wuta
Paul Biya na Kamaru: Shugaban da ya fi tsufa a duniya ya sha rantsuwar kama aiki karo na takwas
Hatsarin mota ya yi ajalin fiye da mutum 1,000 a Nijar a shekarar 2023, fiye da 12,000 sun jikkata