| Hausa
WASANNI
3 MINTI KARATU
Ko Real Madrid za ta bar La Liga?
Rahotanni na cewa Real Madrid tana duba yiwuwar barin gasar La Liga ta Sifaniya don komawa wata babbar gasa a ƙasar Turai.
Ko Real Madrid za ta bar La Liga?
A tarihi ba a taɓa samun wata babbar ƙungiya irin Real Madrid ta bar wata babbar gasa ba. / Hoto: AFP / AFP

Sakamakon yawan rashin jituwa da ake samu tsakanin Real Madrid da hukumar La Liga ta Sifaniya, rahotanni na cewa ƙungiyar na duba yiwuwar barin gasar kacokan.

Real Madrid na tunanin komawa wata babbar gasa a ƙasar Turai, kamar Serie A ta Italiya, ko Bundesliga ta Jamus, ko Ligue 1 ta Faransa.

Wannan batu na zuwa ne bayan da ake taƙaddama kan dacewar jan katin da aka bai wa ɗan wasan gaba na ƙunguyar, Jude Bellingham a wasan da Madrid ta buga da Osasuna ranar 15 ga Fabrairu.

Cecekuce ya ɓarke a wasan da Madrid ta tashi 1-1 da Osasuna, inda alƙalin wasa, Jose Luis Munuera Montero ya bai wa Bellingham jan katin kai-tsaye, bayan ya zargi ɗan wasan da yi masa kalaman zagi.

Alƙalin ya zargi ɗan wasan mai shekaru 21 da yin amfanin da kalaman zagi gare shi a minti na 39, wanda ya janyo ya kore shi nan take.

Sai dai ɗan wasan ya dage cewa ba a fahimci kalaman da ya yi ba saboda fushi, ba wai ga alƙalin ba.

Abu mai wuya

Yayin da ƙungiyar ke nuna matuƙar damuwa kan alƙalanci wasanni a La Liga, shafin Goal ya ambato wata jaridar Sifaniya mai suna Sport na cewa Real Madrid na duba yiwuwar ƙauracewa gasar La Liga.

Sai dai wannan mataki na cewa Madrid za ta bar La Liga, ba zai zo da sauƙi ba, saboda sai hukumomin FIFA, UEFA, da hukumar ƙwallon ƙasar da suke son komawa duka sun amince da sauya sheƙar.

Jan katin da aka bai wa Bellingham ɗaya ne cikin jerin batutuwa da suka ƙona wa Real Madrid a kakar bana.

A farkon watan nan, ƙungiyar ta shigar da ƙorafi ga hukumar ƙwallo ta Sifaniya RFEF, inda ta ce ana samun “mummunar matsalar alƙalanci" bayan da Espanyol ta doke su da ci 1-0.

A halin yanzu, saboda jan katin da aka ba shi da zage-zagen da ya yi, Bellingham na fuskantar dakatarwa da za ta kai ta wasanni tsakanin 4 zuwa 12, wanda zai iya hana shi wasa har zuwa ƙarshen watan nan na Fabrairu.

MAJIYA:TRT Afrika
Rumbun Labarai
Paris Saint-Germain ta lashe gasar Champions League bayan ta lallasa Arsenal a bugun fanareti
Liverpool ta kori kocinta Arne Slot bayan rashin kataɓusa a kakar wasannin nan
Scotland ta buga takardar kudi don murnar kwallon da McTominay ya ci, wadda ta kai su Kofin Duniya
Raphinha ya koka kan masu yawan cewa zai bar Barcelona
Iran ta ce dole Amurka ta ba da biza ga tawagarta ta Kofin Duniya ba tare da la'akari da siyasa ba
Karawar PSG da Bayern Munich za ta sake kayatarwa
Kungiyoyin Gasar Firimiya ta Ingila sun yi asarar dala biliyan 1 na kudin-shiga: Rahoto
Neymar ya yi dambe da ɗan Robinho a haduwarsu ta farko a filin atisaye na Santos
CAF ta tabbatar da ranakun gasar AFCON 2027 a Kenya, Tanzania da Uganda
Iran za ta buga wasannin Gasar Kwallon Kafa ta Duniya a Amurka duk da rikici, in ji FIFA
Tsohon ɗanwasan Nijeriya Eneramo ya mutu sakamakon bugun zuciya yayin wasan sada zumunta
Iran 'ba ta ƙarƙare yanke hukunci' kan halartar Kofin Duniya na 2026 a Amurka ba
Tottenham na neman masanin lafiyar tunani ga ‘yanwasanta, don gujewa fadowa daga gasar Firimiya
'Na yi imanin Arsenal ce za ta ɗaga Kofin Firimiya' - Arsene Wenger
Guardiola ya ce zai sallama Kofin Firimiya idan Man City ta sha kashi a hannun Arsenal
Nijeriya ta yi maraba da 'yarwasan tsere, Favour Ofili wadda aka hana ta sauya kasar da take wakilta
Shugaban FIFA ya ce akwai ‘tabbacin’ Iran za ta halarci Gasar Cin Kofin Duniya
Hukumar FA ta ci tarar Harry Maguire saboda rashin ɗa'a a wasan Man United da Bournemouth
UEFA ta yi watsi da korafin Barcelona kan wasan da Atletico Madrid ta doke su
Masoyin Arsenal ɗan Uganda na barazanar kai Gunners kotu kan damuwar da ya shiga bayan shan kaye