| hausa
DUNIYA
6 MINTI KARATU
'Tsantsar mugunta' — Trump da Musk da Netanyahu sun fito a cikin shirin AI na yadda za a mayar da Gaza
Bidiyon, wanda aka kalle shi sau miliyoyi a Instagram aka kuma yaɗa shi sau dubbai da safiyar Laraba, ya jawo cece-ku-ce a intanet, inda masu sharhi da yawa suka kira shi "mugunta tsantsa" da "wariyar launin fata."
'Tsantsar mugunta' — Trump da Musk da Netanyahu sun fito a cikin shirin AI na yadda za a mayar da Gaza
Trump da Musk da Netanyahu sun fito a cikin shirin AI na yadda za a mayar da Gaza.
27 Fabrairu 2025

Masu amfani da shafukan sada zumunta sun mayar da martani cikin ɓacin rai da ƙorafe-ƙorafe bayan da aka wallafa wani bidiyo na AI a shafukan Donald Trump da ke nuna yadda aka sake gina Gaza da Isra'ila ta lalata zuwa wani wurin shaƙatawa na bakin teku, mai ɗauke da wani mutum-mutumin zinare na shugaban ƙasar Amurka.

Bidiyon, wanda aka kalle shi sau miliyoyi a Instagram aka kuma yaɗa shi sau dubbai a kan shafin sadarwa na Trump na Truth Social da safiyar Laraba, ya jawo cece-ku-ce a intanet, inda masu sharhi da yawa suka kira shi "mugunta tsantsa", "wariyar launin fata" da "son kawar da wasu ƙabilu."

Bidiyon mai tsawon sakan 33 mai taken "Gaza 2025 What's Next?" wato "Gaza a 2025 Mene ne Mataki na Gaba?" ya fara da nuna mutrane a barbaje a kan titi mai ɗauke da tarin ɓaraguzan mutane suna fitowa da kuma masu fitowa daga ramukan ƙarƙashin ƙasa zuwa bakin teku mai bishiyoyi dabino da jiragen ruwa.

Trump ya bijiro da shirin cewa Amurka ta mallaki Gaza wanda a karkashinsa za a kori al'ummar Falasdinawa kuma ba za a bari su dawo ba - shawarar da ta janyo suka sosai.

Daga baya ya bayyana cewa ya sassauta shirin nasa, yana mai cewa shawara kawai yake bayarwa, ya kuma amince da cewa shugabannin kasashen Jordan da Masar sun yi watsi da shawarar da aka ba su ta fitar da Falasdinawa ba tare da son ransu ba.

A cikin bidiyon na dandalin sada zumunta, sautin da aka yi amfani da shi ya hada da wakoki masu taken "Donald's coming to set you free, bringing the light for all to see" wato "Zuwan Donald don 'yantar da ku, ya kawo haske ga kowa da kowa" da kuma wata waƙa mai taken "feast and dance, the deal is done, Trump Gaza number one." "biki da rawa, an yi yarjejeniya, Trump Gaza na daya."

A bidiyon na AI an ga Trump da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ba riguna a jikinsu suna shan lemo, kwance a cikin gadon nan na gefen telu don hutawar masu ninkaya, yayin da wasu hotuna ke nuna abin da ake ganin kamar hamshakin attajirin nan Elon Musk ne yana rawa a cikin ruwan kudi a bakin teku.

Bidiyon ya ƙunshi wasu masu tumbi da gemu suna rawa da kuma hoton shugaban Amurka yana rungumar wani mai ƙaton tumbi da ke rawa.

Shi kuwa Elon Muska an nuna shi yana watsi da daloli yana cin humus a kan rairayin bakin teku.

A wani wajen kuma, an ga wani hoton AI da aka kirkira na Trump da Netanyahu suna shan barasa, wanda aka fara yaɗa shi tun a farkon Fabrairu.

An kuma nuna wani mutum-mutumin zinare na Trump mai girma sosai. Bidiyon ya kuma nuna wani kantin sayar da kayayyakin yin tsaraba da ƙananan mutum-mutumi na Trump a zaune a kan karaga.

Mutane sun yi saurin gano alamu na Littafi Mai Tsarki a cikin bidiyon, inda wani ya ce: "Mai girma Shugaban Ƙasa yayin da nake godiya da abin da kuke yi, kuma ba don kanku kuke yi ba. To godiya ga Ubangiji maɗaukaki, domin in ba don Shi ba, ba za ku iya yin komai ba. Mutum-mutumi alama ce ta Dujjal, don haka ka koma ga Allah."

'An yi ba'a kan bala'in da 'yan Gaza ke ciki'

Bidiyon "abin ban mamaki ne - ganin yadda yake nuna alatu da nishaɗi a ƙasar da yaƙi ya ɗaiɗaita yayin da yake yin watsi da wahalar da miliyoyin mutane ke ciki," in ji wani mai amfani da shafin X Richard Angwin.

"Wannan hasashe ne na abin kunya, ba mafita ba, kuma yana ba'a game da rikicin jinƙai na Gaza. Abin takaici ne."

Howard Beckett, mai fafutuka a Burtaniya kuma ƙwararre a kungiyar kwadago, ya caccaki bidiyon, inda ya kira shi da "tsattsaurar wariyar launin fata da gaske."

"Sai ma an gani sannan za a yarda da abin da na ce: mutum-mutumin Trump; Rawar Musk; Trump da Netanyahu suna wanka a gabar teku da rana suna kuma shan barasa. Mugwaye suna murna da kisan ƙare dangn da suka yi."

Wata Laura Dodsworth a nata martanin a shafin X ta kira bidiyon a matsayin "abun da zai dugunzuma tunani ya saka damuwa."

"Burin ƙwace da wulakanci, da mamaya ne aka nannade da zinari da rashin hankali."

Shi ma wani mai amfani da X ya yi nuni da matakin da Trump ya dauka na tsallaka kan iyaka a shiga ƙasarsa da kuma korar bakin haure da yawa tun bayan hawansa mulki a watan Janairu.

"Abin ban mamaki shi ne Trump ya sanya hannu kan umarnin zartarwa na dakatar da abin da ya kira "mamaya ta haramtacciyar hanya" duk da haka shi kuma yana mamaye wata kasa ba bisa ka'ida ba."

Dokta Shola Mos-Shogbamimu, lauya kuma mai fafutuka, ta bayyana bidiyon a matsayin "shirin kawar da wata al'umma da aka lulluɓe a cikin tsarin harkokin gina gidaje."

"Dan mulkin mallaka, mai tsattsaurar aƙidar girmama farar fata da tsananin son kafa ƙasar Isra'ila.

MAJIYA:TRT World
Rumbun Labarai
COP30: Manyan masu gurbata muhalli na duniya ba su je taron sauyin yanayi na Brazil ba
Rasha ta ce tana sa ido kan Nijeriya bayan barazanar da Trump ya yi ta kai hari kasar
Zohran Mamdani: Matashi Musulmi na farko ya lashe zaɓen Magajin Birnin New York
Yadda amfani da magungunan antibiotic barkatai ya sa cututtuka suka zama makamai
Rundunar Sojin Ruwan Pakistan ta kama mugwayen ƙwayoyi na dala biliyan ɗaya a Tekun Arebiya
An gano sauro a karon farko a ƙasar Iceland
Yadda hukumomi a India suke farautar Musulmai da suke cewa 'Ina son Annabi Muhammad'
Putin ya gargaɗi Trump cewa bai wa Ukraine makamai mai linzamin Tomahawk zai jawo matsala tsakaninsu
Abin da muka sani game da mummunar arangamar kan iyaka tsakanin sojin Pakistan da Afganistan
Waiwayen 1903: An taɓa yi wa Yahudawa tayin Afirka, kamar yadda ake so a mayar da Falasɗinawa yanzu
An naɗa Sarah Mullally mace ta farko Shugabar Cocin Ingila
Yadda mutuwar ɓauna a turmutsutsu ke sauya salon farautar manyan namun dawa
An tsinci gawar jakadan Afirka ta Kudu a Faransa a wajen otal a birnin Paris
Babban Alkalin Kotun Amurka ya dakatar da umarnin Trump na korar ma’aikatan VOA
UNGA: Yadda ta kaya a taron 'nuna wa juna yatsa da huce haushi' na Majalisar Dinkin Duniya
Yadda jami'an diflomasiyyar duniya suka fice daga Zauren UNGA yayin da Netanyahu zai yi jawabi
Jawabin Trump a taron MDD ya fito da sakamakon nuna ƙyamar Musulunci a duniya
An yanke wa tsohon Shugaban Faransa Sarkozy hukuncin shekara biyar a gidan yari
UNGA 80: Trump ya yi alkawarin hana Isra'ila shirin ƙwace Yammacin Kogin Jordan
Ga manyan batutuwa huɗu daga jawabin Sarkin Qatar a taron UNGA