An kashe ɗansanda a kusa da Tehran yayin da zanga-zanga kan matsin rayuwa ta mamaye ƙasar Iran

Tun watan da ya gabata zanga-zanga ta mamaye ƙasar Iran saboda tsanantar lalacewar tattalin arziki.

By
Protesters march in downtown Tehran, Iran, on December 29, 2025. / Reuters

An kashe wani ɗansanda na Iran a wani rikici da ya ɓarke a kusa da babban birnin Tehran, kamar yadda kafofin watsa labarai na cikin gida suka ruwaito a ranar Alhamis.

A cewar rahotanni, an caka wa Laftanar Kanar Shahin Dehghan wuƙa a lokacin zanga-zangar da ta ɓarke a birnin Malard da ke yammacin babban birnin.

Hukumomin tsaro sun ce ana ci gaba da bincike don gano waɗanda ke da hannu a lamarin.

Iran ta fuskanci zanga-zanga tun daga watan jiya wadda ta fara a ranar 28 ga Disamba a babbar kasuwar Tehran, cibiyar harkokin kasuwancin babban birnin, saboda faɗuwar darajar kuɗin Iran da kuma taɓarɓarewar tattalin arziki.

Daga baya zanga-zangar ta bazu zuwa birane da dama a faɗin ƙasar.

Hukumomin Iran ba su fitar da alƙaluman waɗanda suka mutu a hukumance ba.

A halin yanzu, kamfanin dillancin labarai na Tasnim ya ce adadin 'yansandan da suka jikkata a lokacin zanga-zangar ya ƙaru zuwa 568, yayin da kuma wasu 'yansanda 66 na rundunar 'yansanda ta Basij su ma suka jikkata.

Iran ta fuskanci zanga-zanga na tsawon makonni a yayin da take fama da taɓarɓarewar tattalin arziki da kuma faɗuwar darajar kuɗin ƙasar, inda kuɗin ƙasar ya ya faɗi zuwa 1,350,000 a matsayin dala ɗaya a kwanan nan.