Babban jami'in tsaro na Iran, Ali Larijani, ya yi iƙirarin cewa an kama sojojin Amurka, yana zargin Washington da ƙoƙarin ɓoye lamarin.
“An sanar da ni cewa an kama sojojin Amurka masu yawa. Amma Amurkawa suna cewa an kashe su a yaƙi,” kamar yadda Larijani ya wallafa a X a ranar Asabar.
“Duk da yunƙurinsu maras amfani, ba za su iya ɓoye gaskiya ba na tsawon lokaci.”
Sojin Amurka sun ƙaryata ikirarin nan cikin gaggawa, sun ce babu wani sojan Amurka da aka kama.
Wani mai magana da yawun Rundunar Sojin Amurka da ke aiki a Gabas ta Tsakiya da wasu yankunan Asia (CENTCOM) ya shaida wa Al Jazeera cewa ikirarin Iran ba gaskiya ba ne.
“Iƙirarin gwamnatin Iran na kama sojojin Amurka wani misali ne na irin ƙaryarta da yaudara,” in ji mai magana da yawun ga Al Jazeera.
Ƙaruwar tashin hankali a yankin ya biyo bayan hari ta sama na haɗin gwiwa na Amurka da Isra'ila a kan Iran a ranar 28 ga Fabrairu, wanda ya yi sanadin mutuwar fiye da mutane 1,000, ciki har da Jagoran Addini na Iran Ali Khamenei, da fiye da 'yan mata na makaranta 150, da manyan jami'an soja.
Yaƙin ya jawo rashin zaman lafiya a faɗin yankin da kuma hare-haren ramuwar gayya daga Tehran kan wuraren da ke da alaƙa da Amurka a ko'ina cikin yankin.












