Masu kamuwa da cutar HIV sun ragu da kaso 46 cikin 100 a Nijeriya

Dakta Temitope Ilori, Darakta-Janar ta Hukumar Kula da Cutar AIDS ta Kasa (NACA), ta ce a shekarar 2024, an yi wa mata masu juna biyu fiye da miliyan biyar gwajin cutar, a yunƙurin kare jariran da za su haifa daga kamuwa da cutar.

By
Nijeriya ta ce ta samu raguwa a masu kamuwa da cutar HIV / Reuters

Nijeriya ta yi gwajin cutar HIV ga mata masu juna biyu fiye da miliyan biyar a shekarar 2024, wanda wannan babban ci gaba ne a yunƙurin da ake yi na daƙile yaɗuwar cutar daga uwa zuwa jariri.

Dakta Temitope Ilori, Darakta-Janar ta Hukumar Kula da Cutar AIDS ta Kasa (NACA), ta bayyana haka a ranar Litinin yayin wani taro na bikin Ranar AIDS ta Duniya.

Dakta Ilori ta ce jarirai 23,000 da ake zargin suna ɗauke da ƙwayar cutar HIV sun samu gwajin gano cuta tun kafin su kai watanni uku da haihuwa.

“Waɗannan alkaluma suna nuna irin jajircewarmu wajen kare iyaye mata da 'ya’yansu,” in ji ta.

“Sai dai, yawan mata masu juna biyu da ake yi wa gwajin HIV yana kusa da kashi 65%, kuma gano cuta ga jarirai yana kusan kashi 56%. Har yanzu akwai aikin da ya rage.”

A cewar Dakta Ilori, Ranar AIDS ta Duniya ta kasance wani lokaci na tunani, hadin kai, da sabunta kuduri wajen yaki da HIV.

A duniya, mutane miliyan 40.8 ke rayuwa da HIV, inda aka samu mutum miliyan 1.3 da suka kamu da ita a 2024.

Duk da haka, fiye da mutane miliyan 29 yanzu suna samun magungunan rage tasirin cutar a jikin ɗan’adam, alamar ci gaba da nasarar da aka samu ta hanyar hadin kan duniya.

Nijeriya, kamar sauran kasashe da dama, ta fuskanci manyan kalubale a 'yan shekarun nan—daga annobar COVID-19 zuwa matsalolin tattalin arziki da raguwar tallafin wasu kungiyoyi, in ji ta.

Wannan ne ya sa aka zabi taken 2025: “Shawo Kan Matsaloli, Tabbatar da Cigaban Dakile HIV a Nijeriya.”

“Waɗannan matsalolin gaskiya ne, amma ba su sa mun karaya ba,” in ji Dr. Ilori.