| Hausa
NIJERIYA
3 minti karatu
Cocin Katolika a Nijeriya ta rufe makarantu da asibitinta a jihar Benue saboda matsalar tsaro
‘‘Diocesar Katolika reshen Gboko, a jihar Benue, ta bayar da umarnin rufe cibiyoyinta na wucin-gadi a Ihugh wani yanki a karamar hukumar Vandeikya saboda "hare-haren da ake ta kaiwa akai-akai,"
Cocin Katolika a Nijeriya ta rufe makarantu da asibitinta a jihar Benue saboda matsalar tsaro
Cocin Katolika a Nijeriya ta rufe wasu cibiyoyinta a jihar Benue saboda matsalar tsaro

Hukumomin Cocin Katolika reshen Diocese na Gboko, a Jihar Benue ta Nijeriya, sun bayar da umarnin rufe wasu makarantu da asibiti da cocin Ihugh a jihar sakamakon hare-hare da ake yawan kai musu.

Umarnin, wanda aka bayyana a cikin wata wasiƙar coci mai ɗauke da ranar 12 ga Oktoba, ya shafi makarantar sakandaren ’yan mata ta St Winifred, da makarantar firamare da renon yara ta St Winifred, da asibitin St Thomas da kuma cocin St Winifred, duk a ƙaramar hukumar Vandeikya.

Sanarwar wasiƙar ta ce ‘‘ Diocesar Katolika ta Gboko, a jihar Benue, ta bayar da umarnin rufe cibiyoyinta na wucin-gadi a Ihugh wani yanki a karamar hukumar Vandeikya saboda "hare-haren da ake ta kaiwa akai-akai."

Cocin ya kuma bayar da umarnin janye limamai, da mata masu aikin addini da sauran ma’aikatan bishara daga yankin, saboda fargabar tsaron ɗalibai, da malamai, da ma’aikatan lafiya da sauransu.

A cewar cocin, an ƙona ɗakunan kwanan ɗalibai na makarantar sakandaren St Winifred a ranakun 28 ga Oktoba, 2025, da 10 da kuma 15 ga Mayu, 2026, sannan aka sake ƙona su a ranar 11 ga Oktoba, 2026.

Cocin ya kuma ce an sha yin fasa-ƙauri a cocin St Winifred, tare da wasu laifuffuka da aka aikata a asibitin St Thomas.

Hukumomin Cocin sun bayyana cewa sun tattauna da shugabannin al’umma, da sarakunan gargajiya da jami’an tsaro domin neman mafita, amma ƙoƙarin bai samar da tabbacin tsaro na dindindin ba.

Ana zargin matakin rufe cibiyoyin zai shafi damar samun ilimi da kiwon lafiya a yankin.

Cocin ya ce zai taimaka wa ɗaliban da abin ya shafa, don ci gaba da karatu a wasu makarantun Katolika.

Haka kuma, za a tura marasa lafiyar da ke karɓar magani a asibitin St Thomas zuwa wasu cibiyoyin lafiya, tare da tanadin kulawa ta musamman ga waɗanda ke buƙatar agajin gaggawa.

Kazalika hukumomin sun jaddada cewa matakin na da nufin kare rayuka da dukiyoyi, ba wai hukunta al’ummar yankin baki ɗaya ba. Ya ce a shirye suke su koma yankin idan an samar da ingantaccen tsaro.

’Yan sandan Benue sun ce sun fara gudanar da bincike kan lamarin.

Wani rahoto na jaridar Premium Times ya ce kakakin ’yan sandan jihar ya bayyana cewa babu wanda ya rasa ransa a sabon wannan ƙone-ƙone.

Cocin ya yi kira ga shugabannin al’umma, jami’an gwamnati da hukumomin tsaro da su haɗa kai wajen dawo da zaman lafiya tare da hukunta waɗanda aka samu da hannu a hare-haren.