| Hausa
WASANNI
2 minti karatu
Guardiola ya ce zai sallama Kofin Firimiya idan Man City ta sha kashi a hannun Arsenal
Masu sharhi kan gasar Firimiya na cewa wasan na ƙarshen mako tsakanin Manchester City da Arsenal zai fayyace makomar gasar ta kakar 2025-26.
Guardiola ya ce zai sallama Kofin Firimiya idan Man City ta sha kashi a hannun Arsenal
Pep Guardiola shi kaɗai ne manajan da ya taɓa lashe kofin Firimiya sau huɗu a jere. / Reuters

Kocin Manchester City, Pep Guardiola, ya ce kofin Firimiya zai kuɓuce musu idan dai Arsenal ta doke su a wasansu na gaba da za a yi ranar Lahadi mai zuwa.

Gabanin wasan, Arsenal na saman teburi kuma ta ba City tazarar maki shida, duk da cewa City na da kwantan wasa guda, yayin da ya rage makonnin wasa shida a kammala kakar bana.

Da yake jawabi gabanin wasan, Guardiola ya ce, "Idan muka yi rashin nasara [a hannun Arsenal], komai ya ƙare kenan [mun bar musu kofin Firimiya]. Suna da ƙarfi sosai a duka ɓangarori.”

Idan City ta doke Arsenal, hakan na nufin sun cike giɓin maki uku sannan sun karɓi damar kamo Arsenal a hannunsu. Amma Guardiola ya ce kada a ce shikenan su za su ci kofin kai-tsaye.

Ya yi nuni da cewa akwai sauran aiki a gaba kuma ba mai sauƙi ba, kasancewar akwai yiwuwar ɓarar da maki a gaba, musamman ganin irin ƙungiyoyin da za su kara da su.

Ya ce, "Wasanninmu da ke tafe na da haɗari, akwai wasan Everton a gidansu, Bournemouth a gidansu, sannan Aston Villa a ƙarshe a gidanmu. Ga Burnley da Crystal Palace da Brentford a gidanmu.

Masu sharhi kan gasar ta Firimiya na cewa wasan na ƙarshen mako tsakanin Manchester City da Arsenal zai fayyace makomar gasar ta kakar 2025-26.

Baya ga wasan na gaba, hankalin City na kan wasan samifainal na kofin FA da za su kara da Southampton, yayin da Arsenal ke fafutukar lashe kofin Firimiya da kuma na Zakarun Turai inda za su kara da Atletico Madrid a samifainal.