| Hausa
WASANNI
2 minti karatu
Faransa za ta kara da Maroko a wasan farko na zagayen kwatafainal
Wasan tsakanin manyan ƙungiyoyin Turai da Afirka zai zamo wani maimaicin wasan samifainal da ƙungiyoyin biyu suka yi a 2022, inda tawagar Les Bleus suka yi nasara kan tawagar.
Faransa za ta kara da Maroko a wasan farko na zagayen kwatafainal
Didier Deschamps yana shirin kawo karshen wa'adinsa na shekaru 14 mai cike da nasara a matsayin kocin Faransa bayan kammala gasar.

Faransa za ta fafata da Maroko a wani babban wasa wanda shi ne na farko a zagayen kwatafainal na Gasar Kofin Duniya na FIFA 2026.

Bayan kwashe wata guda ana wasanni masu ɗaukar hankali, inda aka zura ƙwallaye 280 cikin wasanni 96, a yanzu tawagogi 48 sun dawo saura takwas kacal, waɗanda ke ƙoƙarin lashe kofin a wasan ƙarshe ranar 19 ga Yuli a East Rutherford.

Faransa, wadda ta fi nuna bajinta a gasar zuwa yanzu, za ta fara zagayen kwata fainal tare da jarumar Afirka, Maroko a filin wasa na Gillette Stadium, a Boston, a wani wasa na maimaicin wanda suka buga a Kofin Duniya na 2022.

Rashin nasara ga tawagar Les Bleus zai kawo ƙarshen tafiyar da jagoran tawagar, Didier Deschamps, wanda zai yi murabus bayan shekaru 14 na nasarori a ƙarshen wannan gasa.

Deschamps, ɗaya daga cikin mutane uku kacal da suka taɓa lashe Kofin Duniya a matsayin ɗanwasa da kuma a matsayin mai horarwa, ya bayyana ranar Laraba cewa bai mayar da hankali kan kafa tarihin kansa ba.

Kocin na Faransa ya yi watsi da damuwar da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta, cewa zaɓin alƙalin wasa ɗan Argentina, Facundo Tello, zai iya jefa tawagarsa cikin matsala.

Faransa da Argentina suna kan hanyar yin karo a wasan ƙarshe a maimaicin fainal ɗin 2022, wanda Argentina ta yi nasara.

Da yake magana kan tawagar Maroko ƙarƙashin jagorancin Mohamed Ouahbi, Deschamps ya ce, “Mun fafata da su shekaru huɗu da suka gabata a samifainal, kuma Maroko ta buga wasan ƙarshe na gasar ƙasashen Afirka”.

Rumbun Labarai
Trump  ya ce ya kira FIFA kan jan katin da aka bai wa Folarin Balogun
Mece ce Doka ta 27 a kundin ladabtarwar FIFA wadda ta ba danwasan Amurka, Balogun damar dawowa wasa?
Neymar ya yi bankwana da tawagar Brazil bayan Norway ta fitar da su daga Kofin Duniya
Nijeriya ta ce an kashe 'yan ƙasarta biyu a zanga-zangar ƙin jinin baƙi a Afirka ta Kudu
Maroko ta kai ga matakin kusa da daf da na ƙarshe a gasar cin kofin duniya yayin da Kanada ta fice
Riyad Mahrez ya yi ritaya daga tawagar Algeria bayan fitar da su daga Kofin Duniya
Ronaldo da Ramos sun ci ƙwallo yayin da Portugal ta doke Croatia a Kofin Duniya
Belgium ta cire Senegal daga Gasar Kofin Duniya ta FIFA 2026
NASA ta sha alwashin aika ƙwallon ƙafa zuwa Duniyar Wata idan Amurka ta lashe Kofin Duniya
Norway ta fitar da Ivory Coast daga Gasar Kofin Duniya
Canada ta fitar da Afirka ta Kudu a zagayen 'yan-32 a Gasar Kofin Duniya
Kun san ƙasashen Afirka tara da suka kai zagayen sili-ɗaya-ƙwale a Gasar Kofin Duniya ta 2026?
FIFA tana cire sunan giya daga Kyautar Gwarzon Wasa da ake bai wa 'yanwasa Musulmi a Kofin Duniya
Antonio Conte ya sake zama kocin Italiya
Wane kasashe biyu ne za su so faduwa wasansu na karshe a rukunin gasar Kofin Duniya?
Cristiano Ronaldo ya zama ɗanwasa na farko da ya zura ƙwallo a raga a Gasar Cin Kofin Duniya shida
Messi ya kafa tarihin yawan cin ƙwallo a Gasar Kofin Duniya yayin da Argentina ta doke Autsria 2-0
Mohamed Salah ya jagoranci Masar a nasararta ta farko a Gasar Kofin Duniya a karawa da New Zealand
Ansu Fati, danwasan Monaco kuma tsohon danwasan Barca, ya zama mawaki
Gasar Kofin Duniya: Mexico ta zama ƙasa ta farko da ta tsallaka matakin sili ɗaya ƙwale