Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci hukumar da ke kula da harkokin man fetur ta Nijeriya da ta ci gaba da bayar da lasisin shigo da man fetur da sauran izinin da suka shafi harkar ga manyan kamfanonin ‘yan kasuwar man fetur guda uku, inda ta ce ƙin yin hakan zai saɓa wa tanade-tanaden Dokar Man Fetur ta Nijeriya wato PIA.
Kamfanonin da lamarin ya shafa sun haɗa da Matrix Energy, A.A. Rano da AYM Shafa.
Mai shari’a Inyang Ekwo ya ce duk wani mataki da Hukumar Kula da Albarkatun Man Fetur ta Nijeriya za ta ɗauka wanda ya saɓa wa dokar man fetur da sauran dokokin da suka dace, zai iya sa duk wani mataki da aka ɗauka game da lasisin shigo da man fetur ya zama ba shi da inganci.
Kamfanonin man fetur ukun ne suka shigar da ƙarar a watan Yuni, inda suka ƙalubalanci yadda hukumar ke tafiyar da batun lasisinsu na shigo da man fetur.
Kamfanonin sun shaida wa kotun cewa sun zuba jarin fiye da dala biliyan 20 samar da kayan aiki da ɓangaren sufuri da sayar da man fetur domin tallafa wa harkokin rarraba man fetur da aka ba su lasisi a faɗin Nijeriya.
Hukuncin ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da shari’a kan shigo da man fetur, yayin da NMDPRA ta amince wa kamfanoni shida shigo da tan 830,000 na man fetur a zangon ƙarshe na shekarar 2026.






















