| Hausa
TURKIYYA
2 minti karatu
Turkiyya za ta bai wa 'yan China izinin shiga kasar ba tare da biza ba
Daga ranar 2 ga Janairu, 'yan China za su samu damar zama a Turkiyya har tsawon kwana 90 ba tare biza ba, matakin da zai haɓaka yawon bude ido da cinikayya tsakanin kasashen biyu.
Turkiyya za ta bai wa 'yan China izinin shiga kasar ba tare da biza ba
The visa-free travel for Chinese tourists is expected to further boost people-to-people connections and deepen bilateral relations. / Reuters
1 Janairu 2026

A hukumance Turkiyya ta ba da izinin shiga ba tare da biza ga 'yan kasar China don yawon bude ido da wucewa, kamar yadda dokar shugaban kasar ta bayyana wacce aka wallafa a ranar Laraba.

Sabuwar manufar da Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya sanya wa hannu, ta bai wa maziyartan kasar Sin damar zama a Turkiyya na tsawon kwanaki 90 a cikin ko wace kwanaki 180, wacce za ta fara aiki daga ranar 2 ga watan Janairun 2026.

Manufar matakin shi ne karfafa huldar yawon bude ido da kasuwanci tsakanin kasashen biyu, biyo bayan karuwar ‘yan China masu shiga Turkiyya.

Alkaluman kididdiga na kasar Turkiyya sun nuna cewa, a shekarar 2024, masu yawon bude ido ‘yan China 410,000 ne suka ziyarci Turkiyya, wanda ya nuna karuwar kashi 65.1 cikin dari idan aka kwatanta da na shekarar da ta gabata.

Yanzu kasar China ta zama daya daga cikin kasuwannin yawon bude ido na Turkiyya da ke saurin bunkasa.

A farkon wannan shekara, jakadan kasar China ya bayyana irin abubuwan da suke jan hankalin ‘yan China zuwa Turkiyya.

"Dumbin abubuwan tarihi, da al'adu, da abubuwan jan hankali da suka shahara a duniya, su ne suke jan hankalin masu yawon bude ido na China zuwa Turkiyya" in ji shi a wani taron da ya gudana a ofishin jakadancin China da ke Ankara.

"Bayan annobar Korona an ga karuwar masu ziyara, kuma Turkiyya ta zama kasuw mafi saurin bunkasa ga baƙi na duniya."

Jakada Jiang ya yi nuni da cewa, ya shaida dadaddiyar wayewar kasar da abubuwan al'ajabi, yana mai jaddada karuwar huldar al'adu da yawon bude ido a tsakanin kasashen biyu.

Jami'ai na sa ran cewa, ba tare da biza ba, zai kara habaka yawon bude ido 'yan China, da tallafawa tattalin arzikin cikin gida, da ƙarfafa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

Dangantakar Turkiyya da China na kara karfafa ta hanyar fadada harkokin kasuwanci, yawon bude ido, da mu'amalar al'adu, tare da karfafa hadin gwiwa a fannin tattalin arziki da diflomasiyya.

Rumbun Labarai
Adadin jama'ar Turkiyya ya kai miliyan 86 a 2025 yayin da jama'ar ƙasar ke ƙara yawa
Matar Shugaban Turkiyya da Sarauniyar Jordan sun ƙara jaddada ƙawance a Istanbul
Turkiyya ta kama jami'an Mossad na Isra'ila biyu a Istanbul kan leƙen asiri
Shugaba Erdogan ya tuna da girgizar ƙasa, ya ce ‘Turkiyya ta cika alkawarinta‘ na sake gina gidaje
Turkiyya ta bunƙasa taimakon da ta ke ba Somaliya na sojojin sama da ƙasa don yaƙi da ta'addanci
Shugaban Turkiyya Erdogan ya gana da Yarima Mai Jiran Gado na Saudiyya Mohammed bin Salman a Riyadh
Shugaban Turkiyya zai ziyarci Saudiyya da Masar a cikin wannan makon
Fidan na Turkiyya ya gargaɗi Amurka kan kai wa Iran hari, ya ce Tehran a shirye take ta tattauna
Zaman lafiyar Iran na da muhimmanci ga tsaron yankin: Turkiyya
Turkiyya da Nijeriya sun ƙudiri aniyar kyautata alaƙar kasuwanci, zuba jari da tsaro
Erdogan da Trump sun tattauna kan Syria da Kwamitin Zaman Lafiya na Gaza
Turkiyya ta goyi bayan Nijeriya a yaƙi da ta'addanci yayin da Erdogan ya karbi baƙuncin Tinubu
Ziyarar Tinubu a Turkiyya: Muhimman abubuwa a tsarin dangatakar Nijeriya
Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Fidan ya gana da takwaransa na Nijeriya Tuggar
Ministan Harkokin Wajen Turkiyya da takwaransa na Nijeriya za su gana kan cinikayya da tsaro
Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hidan ya yaba da "Kwamitin Zaman Lafiya" na Gaza
Turkiyya ta ɗauki dukkan yarjejeniyar zaman lafiyar Gaza da mahimmanci: Erdogan
Fidan na Turkiyya zai halarci bikin sa hannu na 'Hukumar Zaman Lafiya' ta Gaza a Switzerland
An tono makarantar Islamiyya mai shekara 900 yayin aikin sabunta birni a yankin Anatolia a Turkiyya
‘Syria ta ‘yan Syria ce’: Erdogan ya yaba da yarjejeniyar zaman lafiya ta Damascus