Shugabar hukumar ƙwallon ƙafa ta ƙasar Norway ta ce ƙasar ta shirya domin gabatar da ƙorafi a hukumance ga hukumar ƙwallon ƙafa ta Duniya, FIFA, game da jinginar da dakatar da Folarin Balogun na wasa ɗaya a Gasar Kofin Duniya saboda ya saka "wasan gabaɗaya cikin hatsari".
Lise Klaveness, shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta Norway (NFF), ta ce za ta nemi goyon bayan ‘yan majalisarta domin gabatar da ƙorafin ga kwamitin ɗa’a na FIFA game da lamarin da "bai kamata a ce ya faru ba".
Hukumar ta NFF ta riga ta gabatar da ƙorafi a hukumance game da yadda Shugaban FIFA Gianni Infantino ya ba da kyautar zaman lafiya ta hukumar FIFA ta farko ga Shugaban Amurka Donald Trump.
"Zan kawo batun a zaman majalisa domin tattaunawa," kamar yadda Klaveness ta shaida wa The Times a wata hira da aka wallafa ranar Alhamis.
"A gare ni, ya kamata ya kasance a maudu’i ɗaya da ƙorafin ɗa’a."
Tsoma hannun Trump cikin batun Balogun ya janyo ce-ce-ku-ce.
Jan katin da aka bai wa Balogun a wasan ƙarshe na zagayen ƙasashe 32 inda Amurka ta yi nasara kan Bosnia and Herzegovina ya janyo haramta masa wasan ƙasar da Belgium kai-tsaye.
Amma sai FIFA ta shigo ciki kuma ta jingina haramta masa wasan, lamarin da ya janyo suka da yawa, musamman a lokacin da ya bayyana cewa Trump ya shiga lamarin ta hanyar kiran Infantino.
Da alama ce-ce-ku-cen ya bai wa Belgium ƙarin gwiwa kuma ta samu ta lallasa ƙasar da ke cikin masu masauƙin baƙin da ci 4-1.
"Idan ka karkata doka haka, kana kan wata gangara mai tsantsi ne da za ta saka wasan gabaɗaya cikin hatsari," in ji Klaveness.
"Abin damuwa ne ga wasan idan ka saɓa wa dokokin wasan.
"Daga farko, bai kamata a ce ya faru ba. Yana da muhimmanci sosai a halin yanzu a yi tattaunawa ta gaskiya game da shi.
"Dukkanmu mun san wannan hukuncin ya samu tasiri daga wasu daga waje kuma bai samu tsarin da ya kamata ba."
"Muna buƙatar shugabanmu a FIFA ya ce wannan kuskure ne," a cewarta.
'Ƙokarin watsi da lamarin'
Klaveness, wata tsohuwar ‘yar wasan ƙwallon ƙafar Norway wadda ta kasance shugabar NFF tun shekarar 2022, ta bayyana cewa karkata doka domin wani shugaban kasa wani misali ne mai hatsari.
"Idan ka fara sauyawa ta irin wannan yanayin ga shugabannin ƙasashe da siyasar ƙasashe, za ka sauya halayyarka da ta ƙungiyarka, da kuma iyakar da bai kamata shugabannin ƙasashe su shiga ba," in ji ta.
"Kuma abin da ya faru."
Klaveness ba ta ji daɗi ba kuma cewa, a cewar The Times, matakin jingina haramta wasan da shugaban kwamitin ɗa’ar FIFA, Mohammad al-Kamali, ne kaɗai ya ɗauke shi ba tare da tuntuɓar sauran mabobinta ba.
"Idan ka ɗauki matakai masu janyo ce-ce-ku-ce, kuma a lokacin da aka samu wata murya mai ƙarfi daga waje a kunnenka, yana da muhimmanci sosai ka kasance kana da ƙarin muryoyi (da ke yanke hukuncin)," in ji ta.
"Kuma idan ba ka yi ba, kuskure ne."
Klaveness ta ce batun ba abun da za a ƙyale ba ne kawai a manta da shi .
"Ba zai yiwuw a yi ƙoƙarin yin watsi da lamarin ba," kamar yadda lauyar mai shekara 45 ta bayyana.
"Da yawa sun ji wannan... koci=koci da ‘yanwasa da magoya baya... cewa wannan ya yi kusa da yawa da wasan.”


















