Koriya ta Kudu ta nemi yin tattaunawar soji da Koriya ta Arewa don kaucewa rikicin kan iyaka
Seoul ta yi kira da ayi tattaunawar soji ta Korea da nufin rage zaman ɗar-ɗar da kuma fayyace layin kwance ɗamara, bayan sojojin Korea ta Arewa sun ringa tsallake iyaka ba sau ɗaya ba sau biyu ba.
Runduna sojan Koriya ta Kudu ta mika bukata a ranar Litinin ta a yi tattaunawa da Koriya ta Arewa domin kauce wa rikice-rikice a kan iyaka, ta ambato kutsen da sojojin Koriya ta Arewa ke yi a kwanan nan.
"Domin hana ɓarkewar arangama tsakanin soji, rundunarmu ta bayar da shawara a hukumance cewa bangarorin biyu su yi tattaunawar soja tsakanin Koriya domin tattauna kafa wani bayyanannen layin manuniya ga MDL," in ji Kim Hong-cheol, mataimakin ministan manufofin tsaron kasa, a taron manema labarai, wanda yake magan kan layin da ya raba iyakokin kasar na soja.
Kim ya ce sojojin Koriya ta Arewa sun maimaita ketare layin na soja "yayinda suke kafa hanyoyi cikin dabaru, da shingaye, da kuma dasa nakiyoyi".
Sojojin Koriya ta Kudu sun yi harbin gargadi kuma sun yi ta watsawa a rediyo da sauran hanyoyin sanarwa don su tilasta wa sojojin Koriya ta Arewa su ja da baya zuwa bangarensu.
Kim ya ce kutsen na kwanan nan ya faru ne saboda "bacewar mafi yawan alamomin yankin kwance ɗamara" da aka kafa ƙarƙashin Yarjejeniyar Tsagaita Wuta ta 1953 wadda ta kawo dakatar da Yaƙin Koriya.
A zahiri, Seoul da Pyongyang har yanzu suna cikin yanayin yaƙi saboda rikicin ya ƙare ne da tsagaita wuta, ba tare da yarjejeniya ta zaman lafiya ba.
Har yanzu babu amsa
Layin da aka shata yana cikin Yankin Da Aka Kwance wa Damara, wani waje mai faɗin kilomita huɗu wanda yake da tsawon kimanin kilomita 250 (mil 160) a fadin tsibirin Koriya.
Tattaunawar ta soja da ake neman yi ta biyo bayan tayin shugaban Koriya ta Kudu Lee Jae Myung da yi na yin tattaunawa mafi girma Koriya ta Arewa ba tare da wani sharaɗi ba, wanda ke nuna sauyi daga matsayin tsaurin ra'ayi na wanda ya gada.
Tun bayan rantsar da shi a watan Yuni, Lee ya ɗauki matakai da dama don rage zaman tankiya na soja da Koriya ta Arewa mai makaman nukiliya, ciki har da cire lasifukan yada bayanai a kan iyaka da haramta watsa takardun yada labarai masu suka ga Pyongyang.
Har yanzu Pyongyang ba ta mayar da martani ga tayin na Lee ba.
Tsohon shugaban ƙasa Yoon Suk Yeol ya ɗauki salon tsaurin ra'ayi kan Koriya ta Arewa, wanda ya sa ta kusanci Moscow sosai bayan hare-haren Rasha kan Ukraine, abin da ya jefa dangantakar Koriya ta Arewa da ta Kudu cikin ɗaya daga cikin mawuyacin halin da ta taɓa samu a 'yan shekarun nan.
A bara, Koriya ta Kudu da ta Arewa sun shiga wani yaƙin cacakar baka na farfaganda, inda Arewa ta aika dubban balon-balon cike da shara zuwa kudu a matsayin ramuwar gayya ga balon-balon yada bayanai da masu fafutuka daga Koriya ta Kudu suka tura.