Gwamnatin Nijeriya ta ƙaddamar da tallafin jarin N50m ga ɗalibai a fannin ƙirƙire-ƙirƙire

Shirin zai taimaka wajen gano da horar da matasa manyan gobe ‘yan Nijeriya tare da samar da hanyar tallafawa ƙirƙire-ƙirƙirensu masu mahimmaci a fannonin Kimiyya da Fasaha da Injiniyanci da Lissafi da kuma Kimiyyar Lafiya wato (STEMM).

By
Ministan ilimi na Nijeriya

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta kaddamar da shafin neman tallafin jari ga dalibai wato Student Venture Capital Grant (S-VCG) don karfafa wa ƙirƙire-ƙirƙire da dalibai ke jagoranta a faɗin ƙasar.

Matakin na cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Ilimi ta Ƙasar ta fitar a ranar Litinin 17 ga Nuwamban 2025 inda ta ce, gagarumin shirin na daga cikin ƙudurin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na ware tallafin Naira miliyan 50 ga daliban manyan makarantu a Nijeriya da suka ƙirƙiri wani abu sabo da kasar za ta yi alfahari da shi.

Kazalika, shirin zai taimaka wajen gano da horar da matasa manyan gobe ‘yan Nijeriya tare da samar da hanyar tallafa wa ƙirƙire-ƙirƙirensu masu mahimmaci a fannonin Kimiyya da Fasaha da Injiniyanci da Lissafi da kuma Kimiyyar Lafiya wato (STEMM).

Da yake jawabi a wurin ƙaddamar da shirin, Ministan Ilimi na Nijeriya, Tunji Alausa ya jaddada manufar dabarun shirin inda ya ce "Shugaban Ƙasa ya ƙalubalance mu da mu nemi masu basirar ƙirƙire-ƙirƙire da aka taba yi ba a ƙasar daga cikin manyan makarantunmu.’’

“Ba wai kawai muna neman ayyukan ƙirƙire-ƙirƙire ‘yan Nijeriya ba ne; muna neman ɗaliban jami'o'in Nijeriya waɗanda ayyuakansu za a su zama zakaran gwajin dafi a jami'o'inmu da kwalejojinmu’’ in ji ministan, yana mai cewa, wannan zai zama jari mai ɗumbin riba nan gaba ga Nijeriya."

Ma’aikatar ta bayyana cewa dalibai da suka yi nasara za su samu damar cikakken tsarin tallafin wanda ya haɗa da shirye-shiryen horar da ɗalibai sosai, da jagoranci na ƙwararru daga fannin kasuwanci da na masana'antu, da kuma damar amfani da kayan aiki da suke bukata.

Kazalika daliban za su samu kafa da kuma albarkatun da ake buƙata don haɓaka da kuma faɗaɗa sabbin ƙirƙire-ƙirƙirensu, kamar yadda sanarwar ma’aikatar ta bayyana.

An tsara shirin ne don tabbatar da cewa, ba a tsaya iya tallafa wa ayyukan da aka ƙaddamar da su ba ne, amma a jagorance zuwa matakin da su iya shiga kasuwa.