Liverpool ta dakatar da Mohamed Salah daga buga wasanta da Inter Milan

Bayan kakkausar sukar da ɗanwasan Liverpool Mohamed Salah ya yi kan kocinsa Arne Slot, ƙungiyar ta dakatar da ɗanwasan daga buga wasan gaba tare da Inter Milan a gasar Zakarun Turai.

By
Salah na shirin auracewa Liverpool don zuwa buga gasar AFCON da za a fara a Morocco. / Reuters

An dakatar da tauraron ɗan wasan Liverpool, Mohamed Salah daga tawagar ƙungiyar da za ta buga wasan gasar Zakarun Turai da Inter Milan.

Wannan na zuwa ne bayan kalaman da ya yi game da rushewar alaƙarsa da koci Arne Slot.

Ɗanwasan ɗan asalin Masar ba ya cikin jerin ‘yanwasan da Liverpool ta fitar ranar Litinin, duk da cewa an gano shi yana atisaye da tare da tawagar da safiya.

Ranar Asabar ne Salah ya bayyana cewa yana jin kamar Liverpool ta yi "watsi da shi" kuma a yanzu ba shi da kyakkyawar mu’amala da Slot bayan da aka bar shi a benci a karo na uku a jere a wasan da suka yi 3-3 da Leeds.

Mohamed Salah ya yi zargin cewa akwai masu son ganin ya bar Liverpool, inda ya yi barazanar zai iya barin Liverpool ko da a wasansu na gaba da Brighton.

Mafita ga kowa

Sai dai da dama daga jaridun Burtaniya da suka ruwaito dakatar da Salah daga wasan na Talata a Italiya, sun ce ba domin ladabtarwa ba ne, kawai zaɓin ne bai zo kansa ba.

Suna cewa hana Salah buga wasan na gaba wata dama ce ga kowane ɓangare ya samu hutu, musamman ganin lokaci da salon da ɗanwasan ya bi wajen amayar da bain da ke ransa a bainar jama’a.

Sai dai duka da haka, ana hasashen cewa ƙungiyar ba za ta ɗauki matakin ladabtarwa kan Salah ba.

Bayan wasansu da Brighton a ƙarshen makon nan ne Salah zai tafi buga gasar AFCON ta 2025 da za a fara a Morocco ranar 21 ga Disamba.

Mai shekaru 33, Salah shi ne ɗanwasan Liverpool na uku a cin ƙwallo a tarihin ƙungiyar, da ƙwallo 250 a wasanni 420.

Sai dai a baya-bayan nan Salah ya rasa tagomashi yayin da Liverpool ke fama da ƙarfar nasara a wasanninta na gasar Firimiya, inda take mataki na tara a teburi. Kuma ƙwallo huɗu kacal suka ci a wasanni 13.