Shugaban Turkiyya ya naɗa sabon Ministan Shari'a da na Harkokin Cikin Gida
A cewar umarnin, an nada Babban Lauyan Gwanati na Istanbul, Akin Gurlek, a matsayin Ministan Shari'a, inda ya maye gurbin Yilmaz Tunc, yayin da aka naɗa Gwamnan Erzurum, Mustafa Ciftci a matsayin Ministan Cikin Gida, inda ya gaji Ali Yerlikaya.
Turkiyya ta naɗa sabbin ministocin shari'a da na cikin gida bisa umarnin shugaban kasa Recep Tayyip Erdogan da aka sanya hannu a kai kuma aka wallafa a Mujallar Hukuma.
A cewar umarnin, an nada Babban Lauyan Gwanati na Istanbul, Akin Gurlek, a matsayin Ministan Shari'a, inda ya maye gurbin Yilmaz Tunc, yayin da aka naɗa Gwamnan Erzurum, Mustafa Ciftci a matsayin Ministan Cikin Gida, inda ya gaji Ali Yerlikaya.
An yi nadin ne bisa sahe na 104 da 106 na Kundin Tsarin Mulki na Turkiyya.
Bayan sanarwar, Ali Yerlikaya ya tabbatar cewa ya mika Ma'aikatar Cikin Gida ga Mustafa Ciftci kuma ya masa fatan alheri a sabon mukaminsa.
A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafukan sada zumunta, Yerlikaya ya ce ya rike matsayin Ministan Cikin Gida tun 4 ga Yuni, 2023, da amincewar Shugaba Erdogan, kuma ya nuna godiya ga shugaban kasa saboda goyon bayansa a lokacin jagorancinsa.
Har ila yau, ya yi godiya ga ma'aikata a cikin Ma'aikatar Cikin Gida saboda ayyukansu na tabbatar da doka, oda da tsaro, inda ya kammala sakon da fatan alheri ga wanda ya gaje shi.
Haka kuma, Yilmaz Tunc ya fitar da sakon murna bayan nadin Akin Gurlek a matsayin Ministan Shari'a.
Tunc ya ce yi wa Shugaba Erdogan aiki tare da ba da gudunmawa ga tafiyar siyasar jam'iyyar masu mulki ya kasance abin alfahari, yana mai cewa nadinsa a matsayin Ministan Shari'a a watan Yuni na 2023 ya zo da babban nauyi.
Ya jaddada gyare-gyaren da aka aiwatar a cikin shekarun da suka gabata guda 23 a karkashin jagorancin Erdogan don karfafa dimokuradiyya da bin doka, sannan ya ce zai ci gaba da yin aiki domin yi wa ƙasa hidima a wasu mukaman a nan gaba.
Tunc ya kuma taya Gurlek murna tare da masa fatan nasara a sabon mukaminsa.
Nadin sun fara aiki nan take bayan an wallafa su a Mujallar Hukuma.