Kocin tawagar Supera Eagles na Nijeriya, Eric Chelle ya fitar da sunayen ‘yanwasan da za su buga wa Nijeriya wasanni uku a watan Satumba da watan Oktoba.
Jeri na farko daga cikin sunayen ‘yanwasan da aka wallafa a shafukan sada zumunta na tawagar zai buga wasan neman shiga Gasar Kofin Afirka ne da Madagascar ranar 25.
Kazalika ‘yanwasan za su buga wasan neman shiga gasar da Gunie Bissau ranar 29 ga watan Satumba.
Gololi da ke cikin jerin ‘yanwasan su ne Arthur Okonkwo da Maduka Okoye da Stalney Nwabali.
Masu tsaron baya kuma su ne Bruno Onyemachi da Issac James da Benjamin Fredricks da Emmanuel Fernandez da Oluwasemilogo Ajayi da Calvin Bassey da Chibuike Nwaiwu da Bright Osayi Samuel da Olaluwa Aina.
Kazalika jerin ‘yanwasan na da ‘yan wasan tsakiya da suka haɗa da Alexander Iwobi da Frank Onyeka da Wilfred Ndidi da Raphael Onyeka.
‘Yanwasan gaban tawagar su ne Ademola Lookman da Samuel Chukwueze da Moses Simon da Akor Adams da Victor Osimhen da Tolu Arokodare da Goerge Ilehikina da Moses Usor.
Baya ga wannan, Chelle ya fitar da wani jerin sunayen ‘yan wasan kuma da za su buga a wasan da Super Eagles za ta kara da Rasha a ranar 6 ga watan Oktoba.
Gololin da za su buga a wasan a Rasha sun haɗa da Chibuzr Atata da Samuel James da Stanley Nwabali.
‘Yanwasa bayan kuwa su ne Kenneth Igboke da Isaac James da Benjamin Fredricks da Emmanuel Fernandez da Victory Akpe da Bright Osayi-Samuel da Abdullahi Bewane.
A cikin ‘yan wasan tsakiyar tawagar da za ta buga Rashan akwai Wilfred Nididi da Chibuzo Nwoko da Fumen Michael da Gorges Wilfred da Popoola Abdulrasaq da Suleiman Mubarak da Jacob Adeoye da Raphael Onyedika.
‘Yanwasna gaban kuwa su ne Kelechi Iheanacho da Edokpolor Peter da Moses Simon da Akor Adams da Umar Abubakar da Abdullahi Umar.



















