Abin da kallon faɗuwar rana ke yi ga lafiyarka, kamar yadda Kimiyya ta nuna
Abin da kallon faɗuwar rana ke yi ga lafiyarka, kamar yadda Kimiyya ta nuna
Abin da kallon faɗuwar rana ke yi ga lafiyarka, kamar yadda Kimiyya ta nuna
Bincike ya nuna cewa kallon kyawawan abubuwa a cikin yanayi cikin kwanciyar hankali na taimakawa wajen rage damuwa. Hakan na ba ƙwaƙwalwa damar hutawa daga gajiyar tunani, tare da inganta yanayin zuciya.

Ga mutane da dama, faɗuwar rana wani kyakkyawan yanayi ne kawai da ake jin daɗin kallo. Amma ga wasu, lokaci ne na natsuwa, yin tafakkuri da sake duba rayuwa.

Mutane da yawa kan zaɓi wannan lokaci domin yin addu'o'in maraice, yin zikiri ko kuma ɗan hutawa daga hayaniyar rayuwar yau da kullum. Yayin da rana ke nutsewa cikin shafaki, wasu na cewa hakan kan sa su ƙara jin girman ikon Allah da kuma hikimar da ke tattare da tsarin halitta.

Sai dai tambayar ita ce: shin wannan jin daɗin da ake samu daga kallon faɗuwar rana na da wani tasiri ga lafiya?

Masana kimiyya sun ce amsar ita ce e. Amma ba ta hanyar siddabaru ko ikirarin da ake yawan yadawa a kafafen sada zumunta ba.

Rage damuwa da ba ƙwaƙwalwa hutu

Bincike ya nuna cewa kallon kyawawan abubuwa a cikin yanayi cikin kwanciyar hankali na taimakawa wajen rage damuwa. Hakan na ba ƙwaƙwalwa damar hutawa daga gajiyar tunani, tare da inganta yanayin zuciya.

Lokacin da mutum ya tsaya yana kallon faɗuwar rana, yana kuma nisanta kansa daga wayoyi, saƙonni da sauran abubuwan da ke ɗauke hankali. Masana sun ce hakan na iya rage yawan sinadarin cortisol, wanda shi ne babban sinadarin damuwa da jiki ke fitarwa.

Yadda launukan faɗuwar rana ke tasiri

Launukan da ake gani yayin faɗuwar rana, musamman ruwan ɗorawa, ja da ruwan goro, na iya sa mutane da yawa su ji natsuwa da gamsuwa.

Masana ilimin halayyar ɗan Adam sun bayyana cewa ba wai waɗannan launuka suna da ikon warkarwa ba ne, sai dai suna taimaka wa ƙwaƙwalwa ta sassauta aiki tare da mai da hankali ga abin da ke faruwa a wannan lokacin.

Mene ne mindfulness?

Wannan yanayi ne da masana ke kira mindfulness, wato kasancewa cikin cikakkiyar nutsuwa da lura da abin da ke faruwa a wannan lokacin, maimakon damuwa da abin da ya wuce ko fargabar abin da zai zo.

Ɗaruruwan bincike sun nuna cewa yin hakan na taimakawa rage damuwa da fargaba, tare da inganta lafiyar ƙwaƙwalwa.

Fa'idar kasancewa cikin yanayi

Kallon faɗuwar rana a fili, kan tsauni, a bakin ruwa ko kuma a saman bene mai tsayi kan ba mutum damar shaƙar iska mai kyau da kuma mu'amala da kyawawan halittun da ke kewaye da shi.

Masana sun ce kasancewa a wuraren da ke da bishiyoyi, ciyayi ko bakin ruwa na taimakawa rage hawan jini, rage damuwa da kuma inganta lafiyar jiki da ta tunani.

Tasirin faɗuwar rana ga barci

Faɗuwar rana na kuma taimaka wa jiki ya fahimci cewa yini ya ƙare.

Yayin da duhu ke ƙaruwa, ƙwaƙwalwa na fara shirya fitar da sinadarin melatonin, wanda ke taimakawa mutum samun barci mai kyau.

Sai dai masana sun ba da shawarar cewa kada mutum ya koma kallon wayarsa ko kwamfutarsa nan take bayan ya kalli faɗuwar rana, domin shuɗin hasken da sikirin waɗannan na'urori ke fitarwa na iya jinkirta fitar melatonin.

Jin ban mamaki da gamsuwa

Wasu bincike sun kuma nuna cewa kallon abubuwa masu ban mamaki irin su faɗuwar rana na iya ƙara gamsuwa da rayuwa, rage fushi, takaici da juyayi, tare da tunatar da mutum cewa duniya ta fi matsalolinsa girma.

Amma ba magani ba ne

Duk da waɗannan fa'idodi, masana sun jaddada cewa kallon faɗuwar rana ba magani ba ne. Ba zai warkar da cututtuka ko maye gurbin kulawar likita ba.

Sai dai yana iya zama ɗaya daga cikin kyawawan halaye da ke tallafa wa lafiyar ƙwaƙwalwa idan aka haɗa shi da motsa jiki, cin abinci mai kyau, isasshen barci da kuma neman kulawar ƙwararru idan akwai buƙata.

Kammalawa

Lokaci na gaba da rana ta fara faɗuwa, gwada ajiye wayarka na ƴan mintoci.

Ka tsaya. Ka yi dogon numfashi. Ka kalli wannan kyakkyawan lamari da ke alamta ci gaba da tafiyar rayuwa da tsarin halitta.

Wataƙila ba zai warware duk matsalolinka ba, amma binciken kimiyya ya nuna cewa waɗannan ƴan mintoci na natsuwa na iya rage damuwa, inganta yanayin zuciya, taimakawa samun barci mai kyau da kuma ba ƙwaƙwalwa damar hutawa.

Wani lokaci, abubuwa mafi sauƙin yi su ne suka fi amfani ga lafiyarmu.