| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Mutum aƙalla takwas sun mutu, an ceto 26 bayan bene mai hawa uku ya rushe a Legas
Hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Legas (LASEMA) ta bayyana cewa jami'an ba da agajin gaggawa sun samo gawarwaki takwas kuma sun ceto mutum 26 daga ɓaraguzan ginin zuwa misalin ƙarfe 4:20 na yammacin ranar Alhamis.
Mutum aƙalla takwas sun mutu, an ceto 26 bayan bene mai hawa uku ya rushe a Legas
Hukumomi sun ce mutum 8 ne aka tabbatar da mutuwarsu har zuwa safiyar Juma'a. / NEMA / Facebook/NEMA

Aƙalla mutum takwas ne suka mutu, ciki har da wata jaririya yayin da aka ceto mutum 26 bayan wani gini mai hawa uku ya rushe a unguwar Alakija ta jihar Legas ranar Alhamis , kamar yadda hukumomin ba da agajin gaggawa suka bayyana.

Ginin, wanda ya ƙunshi rukunonin shaguna ya rufta ne da misalin ƙarfe 11:40 na safiyar Alhamis, inda wasu mutane da ba a san adadinsu ba suka maƙale a ƙarƙashin ɓaraguzan ginin, kamar yadda Jairdar Premium Times ta ruwaito.

Hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Legas (LASEMA) ta ce zuwa misalin ƙarfe 4:20 da yamma ranar Alhamis jami’ai masu ba da agajin gaggawa sun samo gawarwaki takwas tare da ceto mutum 26 daga ɓaraguzan ginin.

Babban Sakataren na LASEMA, Damilola Oke-Osanyintolu, ya bayyana cewa ana ci gaba da ƙoƙarin ceto, domin ganowa tare da fito da sauran waɗanda lamarin ya shafa.

“Aikin bincike da ceto yana ci gaba har zuwa yanzu,” Kamar yadda Oke-Osanyintolu ya bayyana a wani ƙarin bayani da ya yi.

Bayanai na baya-bayan nan sun nuna ƙari mai yawa kan bayanan da hukumar ta fara bayarwa daga farko..

Oke-Osanyintolu ya bayyana cewa jami’ai daga hukumar LASEMA, da hukumar da ke sa ido a kan gine-gine a jihar (LASBCA) da sauran hukumomi su je wajen domin aikin ceto.

Ya bayyana cewa rahotanni na farko-farko sun nuna cewa wasu masu shaguna da sauran mutane suna cikin ginin a lokacin da ya rufta.

Ruftawar ginin ta haddasa tashin hankali a yankin na kasuwancin mai yawan cunkosn jama’a, inda mazauna da ‘yan kasuwa da masu wucewa suka taru yayin da ma’aikatan agajin gaggawa ke bincika cikin ɓaraguzai domin samun waɗanda suka tsira.

Ana samun ruftawar benaye a jihar Legas mai yawan jama’a da ƙarancin filaye inda son samar da gidaje da yawa ke sa mutane ginin benaye.

Sai dai kuma hukumomi a jihar suna nuna damuwa ga yadda wasu mutanen ke yin biris ga dokokin gine-gine na ƙasar da suka tanadi neman izini kafin a yi gini ko kuma sauya fasalin ginin da aka yi.

A wasu lokutan, hukumomin jihar sukan rusa gine-gine da suke da rauni ko kuma waɗanda aka yi ba bisa ƙa’ida ba, lamarin da ke janyo suka daga mutane da ke ganin yin hakan na haddasa asara ga masu gidajen.