Harin Kasuwar Jilli ba kuskure ba ne – Ministan Tsaron Nijeriya ya kare matakin rundunar soji
Da yake amsa tambaya daga TRT Afrika Hausa, ministan ya bayyana cewa mutanen da aka kai wa harin “duk waɗanda suke wajen ‘yanta’adda ne ko masu hulɗa da su,” yana mai jaddada cewa jami’an tsaro sun yi aiki ne bisa sahihan bayanan sirri.
A yayin babban taron diflomasiyya karo na shida da aka gudanar a Antalya Diplomacy Forum, Ministan Tsaron Nijeriya, Christopher Gwabin Musa, ya kare matakin sojojin ƙasar kan harin da aka kai a Kasuwar Jilli, yana mai cewa ba kuskure aka yi ba kamar yadda wasu ke zargi.
Da yake amsa tambaya daga TRT Afrika Hausa, ministan ya bayyana cewa mutanen da aka kai wa harin “duk waɗanda suke wajen ‘yanta’adda ne ko masu hulɗa da su,” yana mai jaddada cewa jami’an tsaro sun yi aiki ne bisa sahihan bayanan sirri.
Ya ce, “Abin da ya faru a Jilli ba kuskure ba ne… duk wanda yake tare da su shi ma ɗaya ne,” yana mai gargadin al’umma da su guji bai wa ‘yan ta’adda kowace irin gudunmawa, ko da ta hanyar kai musu abinci ko magunguna.
Ministan ya ƙara da cewa irin wannan hulɗa da ‘yan ta’adda na taimaka musu su ci gaba da aikata laifuka, yana mai cewa, “Idan mutane suka daina kai musu abinci… wannan abin zai kare gaba ɗaya.”
Dangane da zargin yawaitar kuskuren hare-haren sama da ke shafar fararen hula, ya musanta cewa hakan na faruwa a halin yanzu, yana mai cewa tun bayan abin da ya faru a Tudun Biri, ba a sake samun irin wannan kuskure ba.
A wani ɓangare na tattaunawar, Ministan ya ba ‘yan Nijeriya tabbacin cewa gwamnati da jami’an tsaro na iya bakin ƙoƙarinsu wajen tabbatar da zaman lafiya, amma ya jaddada muhimmancin haɗin kan al’umma.
Ya ce, “Jami’an tsaro su kaɗai ba za su iya yi ba… mutane su dinga ba mu bayanai idan sun ga wani abu marar kyau.”
Haka kuma, ya bayyana cewa gwamnati na ci gaba da samar da kayan aiki da goyon baya ga jami’an tsaro, yana mai kira ga ‘yan ƙasa da su haɗa kai da gwamnati domin kawo ƙarshen matsalar tsaro a ƙasar.
Dangantakar Nijeriya da Turkiyya na ƙara ƙarfi
A ɓangaren dangantaka da ƙasashen waje, musamman Turkey, Ministan ya bayyana cewa ziyarar da suka kai taron a Antalya na nuna yadda shugabannin Nijeriya ke ƙoƙarin ƙarfafa alaƙa domin inganta tsaro.
Ya ce wannan ita ce ziyara ta biyu a cikin ‘yan watanni, bayan wadda aka kai a watan Janairu tare da shugaban ƙasa, inda aka fara tattaunawa kan ƙara haɗin gwiwa.
A cewarsa, “Shugaban ƙasarsu tun da muka zo ya tabbatar da duk abin da muke so na kayan aikin yaƙi… duk zai ba mu,” yana mai nuni da yadda Turkiyya ke nuna goyon baya ga Nijeriya.
Ministan ya bayyana cewa an riga an daɗe ana sayen kayayyakin soji daga Turkiyya, ciki har da motocin yaƙi irin su APC da MRAP, da kuma jirage masu saukar ungulu. Ya ƙara da cewa yanzu ana shirin faɗaɗa wannan haɗin gwiwa.
A wani sabon mataki kuma, Nijeriya na shirin haɗa kai da Turkiyya wajen ƙera kayayyakin tsaro a cikin gida, inda ya ce, “Za mu jawo su su zo Nijeriya mu ƙirƙiri kayan da muke buƙata… za mu ƙera bindigogi da alburusai da sauran kayayyakin aiki.”
Ya bayyana cewa wannan mataki zai taimaka wajen rage dogaro da waje tare da ƙarfafa ƙoƙarin da ake yi na kawo ƙarshen matsalar tsaro a Nijeriya.
A ƙarshe, Ministan ya jaddada cewa haɗin gwiwar da ke tsakanin Nijeriya da Turkiyya na da muhimmanci wajen cimma burin zaman lafiya, yana mai cewa za su ci gaba da aiki tare har sai an samu cikakken tsaro a ƙasar.