Kwamitin Zaman Lafiya na Duniya zai gabatar da shirin farfado da Gaza na dala biliyan $2.45: Rahoto

Shirin ya ƙunshi tanadin kuɗaɗen samar da matsugunan wucin gadi, kwashe baraguzan gine-gine, gyaran asibitoci, farfaɗo da tattalin arziki, da kuma tura rundunar tsaro ta ƙasa da ƙasa.

By
Kwamitin Zaman Lafiya zai gabatar da shirin farfado da Gaza na dala biliyan $2.45: Rahoto / Anadolu Agency

Kwamitin Zaman Lafiya (Board of Peace) zai gabatar da wani shirin farfado da Gaza bayan yaƙi, wanda zai ɗauki tsawon watanni shida tare da kashe dala biliyan 2.45, a wani taro da zai gudana ranar Laraba, a cewar rahoton Axios.

Shirin mai kunshe da ayyuka 66, ya samo asali ne daga shawarwarin da mutane da dama da ke wakiltar ƙasashe 28 da ke cikin Kwamitin Zaman Lafiya, da kuma gwamnatin Falasɗinawa ta ƙwararru, suka bayar tsawon shekara guda.

Shirin ya ƙunshi tanadin kuɗaɗen samar da matsugunan wucin gadi, kwashe baraguzan gine-gine, gyaran asibitoci, farfaɗo da tattalin arziki, da kuma tura rundunar tsaro ta ƙasa da ƙasa.

“Shirin ya nuna yadda za a kafa gwamnati daga tushe, farfaɗo da tattalin arzikin da ya ruguje, da kuma farfaɗo da yankin da ya fuskanci bala'i,” wani jami'in Kwamitin Zaman Lafiya ya bayyana.

An kafa Kwamitin Zaman Lafiya ne a watan Janairu a matsayin wani ɓangare na babban shirin zaman lafiya na Gaza na Shugaban Amurka Donald Trump, wanda shi ne shugaban kwamitin.

Ƙudurin Majalisar Ɗinkin Duniya mai lamba 2803 ne ya amince da shirin, wanda aka ɗora wa alhakin sa ido kan sauyin Gaza, ciki har da harkokin mulki, tsaro da sake gina yankin.

Tun daga ranar 8 ga Oktoba, 2023, Isra'ila ta kashe sama da Falasɗinawa 73,000, tare da jikkata fiye da 174,000, a yaƙin da ake yi a Gaza, yayin da kusan kashi 90 cikin 100 na ababen more rayuwa a yankin suka lalace ko suka ruguje.