Gobara ta ƙona Masallacin Shitta-Bey da ke Lagos wanda ke da alaƙa da Daular Usmaniyya ta Turkiyya
Wata gobara mai ban-ala'jabi da ta lalata wani yanki na masallacin Shitta-Bey na iyalan Animashaun da ke birnin Lagos, wanda ke da alaƙa da Daular Turkiyya.
A ranar Talatar nan ne wata gobara mai ban-ala'jabi ta tashi a sanannen Masallacin Shitta-Bey na iyalan Animashaun da ke birnin Lagos a Nijeriya.
Gobarar ta fara ne da sanyin safiya, kuma ta lalata wani sashen gidan, wanda ya haɗa da daɗaɗɗen masallacin da a baya gwamnatin Lagos ta ayyana a matsayin cibiyar tarihi.
Wutar ta kuma shafi gidan iyalan sanannen jigo a tarihin Musulunci a yankin Lagos, wato Animashaun.
Rahotanni daga Lagos na cewa lamarin ya sake haifar da damuwa kan amincin wasu wuraren tarihin addinin Musulunci a yankin, musamman Masallacin Alli-Balogun Wasinmi mai shekaru fiye da 100.
Jaridar The Nation ta ambato Mataimakin Shugaban Ƙungiyar Zuriyar Alli-Balogun, Dr. G.T. Alli-Balogun, yana bayyana gobarar a matsayin asara ga al’ummar Musulmin Lagos.