Laifi mafi munin: AU ta nemi MƊD ta ɗauki mataki kan biyan diyyar cinikin bayi bayan MƊD ta tabbatar

Kungiyar Tarayyar Afirka ta ce ta jajirce domin aiki da Majalisar Ɗinkin Duniya domin tabbatar da adalci a tarihi bisa ƙudurin majalisar.

By
Miliyoyin maza da mata da kananan yara ne aka tura nahiyar Amurka a jiragen ruwa daga ƙarni na 16 zuwa na 19 don aiki a wani yanayi na tsananin wahala / AA

Ƙungiyar Tarayyar Afirka ta yi maraba da ƙudirin Majalisar Ɗinkin Duniya (MƊD) mai muhimmanci wanda ya ayyana cinikin bayi daga Afirka zuwa Turai da Amurka da kuma bautar da ‘yan Afirka a matsayin “laifi mafi muni kan bil’adama,” inda ta bayyana matakin a matsayin muhimmin mataki na duniya zuwa amincewa da rashin adalcin da aka yi a tarihi.

Shugaban Hukumar Ƙungiyar Tarayyar Afirka, Mahmoud Ali Youssouf, a wata sanarwa da ya fitar ya ce amincewa da ƙudiri mai lamba A/80/L.48 wani muhimmin mataki ne na ƙoƙarin da aka daɗe ana yi na son tabbatar da tasirin cinikin bayi da ya daɗe.

“Wannan matakin mai cike da tarihi wani babban ci gaba ne zuwa tabbatar da gaskiya da adalci da kuma samun waraka, kuma ya ƙarfafa buƙata ta gaggawa da ake da ita ta magance tasirin cinikin bayi da ya daɗe,” in ji shugaban hukumar.

Ta ƙara da cewa za ta ci gaba da neman duniya ta amince da kuma fayyace gaskiya yayin da ta ke nanata kiranta na “cikakkiyar amincewa da tasirin cinikin bayi na tarihi da kuma na yanzu, ciki har da neman adalci na biyan diyya.”

Jerin ƙarni na laifi

Yammacin Afirka da Tsakiyar Afirka sun sha wahala da matsalar cikin bayi zuwa Turai da Amurka, wadda daga ƙarni na 16 zuwa na 19 ta sa aka tura miliyoyin maza da mata da ƙananan yara a cikin jiragen ruwa zuwa nahiyar Amurka don ayyuka a wani hali mai tsananin wuya -- wanda ke yawan janyo rasa rayuka.

A cikin da yawa daga cikin waɗannan ƙasashen, baƙaken fata na ci gaba da fuskantar wariya da talauci a yau.

Ƙudirn wanda , ƙasar Ghana, ta jagoranta a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ya samu karɓuwa inda ƙasashe 123 suka amince da shi. Ƙudirin ya tabbatar da irin tarin yawan da kuma cin zarafin da tasiri na tsawon lokaci da cinikin bayi zuwa Turai da Amurka ya yi , ciki har da wariyar launin fata da ke ci gaba da kuma rashin adalci.

Ƙungiyar Tarayyar Afirka ta yaba wa shugabancin Ghana, tana mai cewa matakin “ya nuna kiran na aƙida da Afirka ta daɗe tana yi da samun cikakken amincewa na faruwar cinikin bayi da kuma tasirinsa mai daɗewa.”

“Ƙungiyar Taryyar Afirka tana jajircewa domin aiki da MƊD, da ƙasashe mambobin majalisar da kuma abokan aiki domin inganta adalci a tarihi da kuma tabbatar da cewa ba a manta da irin waɗannan laifukan ba ko kuma sake maimaita su.”

Martanin duniya

Duk da muhimmancinsa a matsayin wata alama, ƙudirin ya fitar da rarrabuwar kawuna a tsakanin ƙasashen duniya.

Amurka da Isra’ila da Argentina sun ƙi amincewa da ƙudirin, yayin da wasu ƙasashe 52 suka ƙi ƙada ƙuri’a. Masu suka, ciki har da Faransa sun ce bayyana cinikin bayi zuwa Turai da Amurka a matsayin laifi “mafi muni” na “barazanar gwara kan wani bala’i na tarihi da wani bala’i na tarihi".

A kan titunan Accra, kuwa, halin murna ake ciki, inda mutane da dama ke ganin lamarin a matsayin abin da ya kamata an daɗe da amincewa da shi.

“Ba kawai wani lokaci mai cike da tarihi ba ne a gare mu a matsayin ƙasa, ya kuma tabbatar da wahalar da kakanninmu suka sha tare da buɗe ƙofa wa adalci,” kamar yadda wata daliba ‘yar Ghana, Abigail Selikem, ta shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP.

A ƙasar Benin mai maƙwabtaka, martanin mutane ma ya mayar da hankali ne kan abin da ya kamata ya biyo baya. “Wannan ƙuri’ar da aka ƙada ta ba mu damar iya ambatar abubuwa ba tare da tsoron ramuwar gayya ba. Mataki na gaba shi ne , ina fata, kira mara iyaka ga biyan diyya,” in ji marubuci Ousmane Aledji.

Wasu kuwa suna shakkar ko tabbatar da abin da ya faru ƙadai zai iya kawo sauyi mai ma’ana. “Tabatar da shi na da kyau, amma ya kamata mataki da za a iya gani ya biyo baya,” in ji wani ɗan Benin kuma ɗan kasuwa mai shekara 42, Larissa Adjivon.